Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya ce akwai rashin tunani a likitocin da ke neman a gyara masu tsarin biyan albashin CONMESS, sannan a biya su ariyas na tsarin albashi tun daga 2014.
Likitocin waɗanda ke cikin Ƙungiyar Likitocin Cikin Gida ta (NARD), sun bayar da wa’adi a ranar Asabar cewa a biya su dukkan ƙarin albashin su da kuɗaɗen ariyas, tun daga 2015.
Sannan kuma sun nemi a biya su kuɗaɗen alawus ɗin horaswa na 2023, wato MRTT.
Idan ba a biya su ba nan da makonni biyu, to za su tafi yajin aikin da ba su san ranar komawa bakin aiki ba.
Sun kuma yi tir da wani ƙudirin da ake neman amincewa da shi a majalisa, wanda ake ƙoƙarin kafa dokar da ta hana likitoci fita waje, har sai sun yi tsawon shekaru biyar su na aiki a Najeriya kafin su tsere zuwa ƙasashen waje.
Minista Ngige ya maida masu raddin cewa likitocin ba su da godiyar alherin da wannan gwamnatin ta masu.
Ya ce sun wuce makaɗi da rawa wajen neman ƙarin albashi da kuɗaɗen alawus.
‘Ni Ma Albashi Na Ya Yi Min Kaɗan, Bai Kai Naira Miliyan 1 A Wata Ba’ – Minista Ngige:
A wata tattaunawa da Ngige ya yi da gidan talabijin na Channels dangane da Ranar Ma’aikata, ya ce shi kan sa a matsayin sa na Minista albashin da ake biyan sa duk wata bai kai naira miliyan ɗaya ba.
Ngige ya ce Naira 942,000 ake biyan sa a wata. Kuma a cikin kuɗin zai fitar da albashin hadimin sa, sannan kuma ba shi da wani alawus, sai da idan ya yi wata tafiya a waje, to shi ne za a biya shi Naira “100,000, Ƙaramin Minista kuma kuɗin alawus-alawus ɗin tafiye-tafiye na sa Naira 75,000 ne.”
Makonni biyu da su ka gabata, shi ma Karamin Ministan Ƙwadago, Festus Keyamo, ya bayyana cewa, “na fi samun kuɗi a sana’ar lauya fiye da abin da ya ke samu a matsayin minista.
“Kai bari ma na faɗa da babbar murya, ni fa aikin lauya da harkar dillancin gidaje ya fi min samun kuɗaɗe fiye da riƙe muƙamin minista. Ta yaya za a ce babban lauya kama ta da ya shafe shekaru 30 ina aikin lauya da harkar kadarori da shiga tsakanin masu husuma a duniya ina samun kuɗi, amma a riƙa yi min kallon wai ban isa mallakar gida a Amurka ba?, inji Keyamo cikin raddin da ya mayar wa masu surutai bayan ya watsa wani bidiyon sa a tiwita, inda aka nuno shi a gidan sa da ke Amurka ya na zaune da kayan motsa jiki, inda ya ke hutu a can.
Ƙaramin Ministan Ƙwadago Festus Keyamo, ya maida wa masu sukar sa kakkausan raddi kan yadda ya mallaki gida a Amurka.
Lamarin dai ya faru ne bayan da ya watsa wani bidiyo a ranar Asabar, inda aka nuno shi ya na shaƙatawa a gidan sa da ke Amurka.
Masu suka da adawa da dama sun riƙa tambayar yadda aka yi ya mallaki gida Amurka.
Keyamo ya ce masu sukar sa ba su da ƙoshin tarbiyya da sanin ya kamata.
Ya ce ya mallaki kadarori a Amurka, ciki kuwa har da gidan da aka nuno shi a ciki ya na hutun shaƙatawa a Amurka.
Ya ce ya kwashe sama da shekaru 30 ya na neman kuɗi a aikin lauya, ba a cikin Najeriya kaɗai ba, har a ƙasashen waje.
“Kai bari ma na faɗa da babbar murya, ni fa aikin lauya da harkar dillancin gidaje ya fi min samun kuɗaɗe fiye da riƙe muƙamin minista. Ta yaya za a ce babban lauya kama ta da ya shafe shekaru 30 ina aikin lauya da harkar kadarori da shiga tsakanin masu husuma a duniya ina samun kuɗi, amma a riƙa yi min kallon wai ban isa mallakar gida a Amurka ba?, inji Keyamo cikin raddin da ya mayar wa masu surutai bayan ya watsa wani bidiyon sa a tiwita, inda aka nuno shi a gidan sa da ke Amurka ya na zaune da kayan motsa jiki, inda ya ke hutu a can.
“Tun kafin na zama minista na tara kuɗaɗen da na sayi gidaje. Ya ce kuma ya fara bayyana wa Hukumomo kadarorin sa tun ma a shekarar da aka naɗa shi mamba a Hukumar NDIC.
Ya ce kuma dukkan kadarorin sa na da rajista a Hukumar CCB.
“Kuma a cikin fam ɗin da na bayyana kadarori na, duk na rubuta asusun ajiya ta na bankunan waje, da adadin kuɗaɗen da ke cikin kowane asusun. Na yi haka a lokacin da aka naɗa ni Minista, cikin 2019.
“Kuma cikin 2021 na sai da na rubuta wa hukumomin da abin ya shafa, na ce masu ina so na kwashe kuɗi na da ke waje ajiye a asusun banki, zan sayi kadarori da kuɗaɗen, maimakon na bar su ajiye a banki.”
Ya ce mutane da dama sun raina shi, gani su ke yi bai cancanci mallakar kadarorin ba.
Discussion about this post