Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa Ɗangote ya kusa gama biyan bashin kuɗaɗen da ya ramta don aikin ginin matatar mai wadda aka ƙaddamar.
Emefiele ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi wurin buɗe katafariyar matatar ɗanyen mai ta Aliko Ɗangote, a Legas, ranar Litinin.
CBN ya taimaka da bayar da kuɗaɗe har naira biliyan 125 domin gudanar da ayyuka da saye-saye ko buƙatun cikin gida Najeriya, a lokacin da ake gudanar da aikin.
Emefiele ya ce CBN ta kai ɗauki a matsayin ɗaya daga cikin irin goyon bayan da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi wajen ganin masu zuba jari sun faɗaɗa hanyoyin bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.
“Abin da ba a ma sani ba shi ne Dangote ya fara biyan wasu basussuka da ya karɓa kafin ma a buɗe masana’antar tace ɗanyen man.
“Hakan ya nuna irin namijin ƙoƙarin Dangote da kamfanonin da ke ƙarƙashin sa. Ina farin cikin shaida maku cewa zuwa yau bashin da ake bin Ɗangote a kan aikin gina wannan matata, ya ragu sosai daga sama da dala biliyan 9, ya dawo dala biliyan 2.7.” Inji Emefiele.
A na sa jawabin, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Matatar Fetur ta Ɗangote za ta sauya fasalin tattalin arzikin Najeriya ɗungurugum.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana Matatar ta wadda ya buɗe a Legas, cewa za ta sauya ci gaba da tattalin arzikin Najeriya ɗungurugum, kuma za ta bunƙasa harkokin fetur, ba a Najeriya kaɗai ba, har ma Afrika baki ɗaya.
Shugaba Buhari ya buɗe Matatar Fetur ɗin a Ijebu-Lekki, Legas, wadda ake kyautata wa yaƙini da tabbacin wadatar da Najeriya fetur ɗin da ta ke buƙata a kullum, har ma a riƙa fitarwa ƙasashen waje.
Sanarwar da Kakakin Shugaban Ƙasa ya fitar, Femi Adesina ya ce Buhari ya yi furucin ne a lokacin da ya ke buɗe matatar fetur ɗin, a ranar Litinin.
Shugabannin ƙasashen Ghana, Togo, Nijar da Sanagal duk sun halarta. Chadi ma ta aiko wakilin shugaban kasar su ya halarta.
“Wannan katafariyar masana’anta da mu ke buɗewa a yau, babban misali ne na abin da za mu iya cimma idan aka ƙarfafa wa masu zuba jari guiwa, ta hanyar bunƙasa kasuwancin su domin haɓɓaka tattalin arzikin Najeriya.” Inji Buhari.
“Ina da yaƙinin cewa wanda zai gaje ni, Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, zai ci gaba da inganta tattalin arzikin ƙasa ta hanyar ƙarfafa wa manyan masu zuba jari, domin tattalin arziki ya bunƙasa.
“Ina matukar farin ciki zan bar tattalin arzikin Najeriya a hannun wanda ya dace kuma ya cancanta ya kula da shi sosai da sosai.”
Buhari ya jinjina wa Aliko Ɗangote, wanda ya kafa matatar da za ta iya tace ganga 650,000 a
Kowace rana.
Daga nan ya shawarci sauran manyan ‘yan kasuwa da masu zuba jari su kwaikwayi irin hoɓɓasar da Dangote ya yi.