Wani magidanci mai suna Oyeyimks Adegoke a ranar Juma’a ya roki kotu dake Mapo a garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo ta raba auren sa da matarsa Wuraola saboda yana zargin tacewa ita matsafiya ce.
Adegoke ya ce tun da ya auri Wuraola ya samu karayar arziki.
Ya ce baya ga tsafi Wurola na da taurin kai da rashin biyayya ga ni mijinta.
“A kwanakin baya Wuraola ta yi wa motocina biyu da babur daya da nake kabu-kabu da su tsafin da dukan su suka lalace.
“Ta Kuma lalata motar da na bata kyauta domin ta rika samun kudi da shi. Sannan Wuraola ta rika zubar da duk cikin da na yi mata.
“A dalilin haka nake so kotu ta raba aure na da ita saboda na gaji da zama da ita.
Alkalin kotun Mrs S.M. Akintayo ta ce za a ci gaba da shari’a ranar 29 ga Yuni domin Wuraola ta samu damar gabatar da nata shaidun.
Discussion about this post