Wani magidanci Musibau Oseni ya roki kotu dake Mapo a Ibadan da ta raba kullin airen dake tsakanin sa da matarsa Afsat saboda kiyayya da rake masa.
Oseni ya ce ya auri Afsat shekaru 19 da suka wuce amma ya ce tun da Afsat ta ga ya samu kararyar arziki ba kaman da ba ta fara nuna masa kiyayya, ta nesanta kanta da shi.
“Na fara samun matsala da Afsat lokacin da aka saka dokar hana walwala saboda cutar Korona, a lokacin ne harkoki suka tsaya min cak.
“ Tun daga wannan lokaci wulaƙanci yau da ban da na gobe, don bani da kuɗi. Da ta gaji sai ta kwashe kayanta ta bar daga gidana.
“Dole in hakura da auren Afsat saboda kawai ya nuna dai ashe ta an sona ne saboda abin hannuna a tsawon shekarun da muka yi aure. Da yanzu ba ni da shi karta min rashin mutunci kawai take yi babu kakkautawa.
Alkalin kotun Mrs S.M. Akintayo ta dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 28 ga Yuni domin Afsat ta samu daman gabatar da nata shaidun a kotu.