A kotun dake Igboro ta Tsakiya a Ilorin jihar Kwara ne wani magidanci mai suna Ibrahim Omo-Alijana ya kai karar matarsa Kudirat inda ya roki kotu ta raba auren dake tsakanin sa matar sa saboda tsananin taurin kai da rashin kunya da take masa.
Sai dai kuma a zaman da kotun ta yi ranar Talata Kudirat ta roki kotun da kada ta raba auren cewa tana son mijinta kuma ba za ta iya zama ba tare da shi ba gashi kuma har sun haihu ya’ay shida.
A hukuncin da ya yanke alkalin kotun AbdulQadir Umar ya bai wa ma’auratan shawarar su sassanta kansu, cewa zaman auren ya fi rabuwan da suke so su yi.
Umar ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 12 ga Yuli.
Haka kuma a wata shari’ar matar aure mai suna Bolanle Abdullahi ta kai karar mijinta Abdullahi Yahaya kotu yayin da take neman kotun ta warware aurenta na shekara 11.
Bolanle ta ce tana so ta rabu da mijinta saboda ba ta son shi.
Yahaya ya roki kotun kada ta raba auren saboda yana son matarsa.
Ya ce Bolanle ta garzaya kotu domin kotu ta raba auren su bayan sun samu rashin jituwa a tsakanin su.
Yahaya ya roki kotun ta bashi damar sassantawa da matarsa
Sai dai kuma duk da rokon da Yahaya ya yi, Bolanle ta ce ta gaji da zama da mijin nata, a raba auren kawai kowa ya huta.
Alkalin kotun Umar ya bai wa ma’auratan damar sassanta kansu sannan ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 12 ga Yuli.
Discussion about this post