Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ƙaryata raɗe-raɗi da ji-ta-ji-tar cewa bankin zai janye sabbin Naira 1000, N500 da N200 daga hannun jama’a da bankunan kasuwanci.
CBN ya ce maganganun duk ƙarairayi ne ba gaskiya a ciki. Ya ce kawai dai wasu marasa kishi ne ke ƙoƙarin jefa tsoro da firgici a zukatan jama’a, ta yadda su kuma za su cimma wata ɓoyayyar manufar su.
Cikin wata sanarwa da CBN ya fitar ya ce kuɗaɗen na nan ana ci gaba da magani da su, kuma yanzu haka ana ɗibar su daga Kamfanin Buga Kuɗi na Ƙasa (NSPMC).
CBN ya ce zai ci gaba da ƙara ingizo kuɗaɗen a cikin jama’a domin a ji sauƙin hada-hadar bunƙasa tattalin arzikin ƙasa a cikin sauƙi.
Daga nan bankin ya shawarci ‘yan Najeriya su yi biris da duk wata ji-ta-ji-ta mai nuna cewa wai za a janye sabbin kuɗaɗe daga hannun jama’a da bankunan kasuwanci.
Cikin Disamba ne aka ƙirƙiro sabbin kuɗaɗen, waɗanda fara amfani da su ya haddasa kusan durƙushewar harkokin kasuwanci da sauran harkokin yau da kullum a ƙasar nan.
Maganar za a janye sabbin kuɗi ji-ta-ji-ta ce, ba gaskiya ba ce.