Tabbatattun bayanai sun nuna cewa wasu gwamnoni masu barin gado ba za su samu damar yin hutun hutawa daga jidali da wahalhalun gudanar da mulki, bayan sun sauka a ranar 29 Ga Mayu ba.
Alamomi na nuni da cewa wasu su a kurkukun tsare waɗanda ake zargi da danne kuɗaɗen talakawan da aka ba su amana za su yi na su hutun, a ofishin EFCC.
Dalili shi ne, Hukumar EFCC ta fara wani gagarumin binciken gwamnoni da mataimakan su, waɗanda da yawan su laƙanin rigar sulken da garkuwar kariyar su zai daina aiki ya karye a ranar 29 Ga Mayu.
PREMIUM TIMES ta ci karo da wani kwafen takarda mai nuni da cewa EFCC ta fara bin-diddigin gwamnoni 28 da mataimakan su, domin ƙwato haƙƙin talakawa da ake zargin sun sata ko sun jida, ko sun karkatar.
Akwai gwamnoni 18 da mataimakan su waɗanda EFCC ke bincike, kuma za su sauka a ranar 29 Ga Mayu.
Ɗaya daga cikin su, Bello Matawalle na Zamfara, zai sauka bayan ya yi zango ɗaya kaɗai, sauran 10 kuwa za su sauka ne bayan sun kammala wa’adin su na shekaru takwas kan mulki.
PREMIUM TIMES ta dafe wasiƙar da EFCC ta yi wa Hukumar CCB, inda ta nemi a ba ta kwafen bayanan kadarorin da kowane gwamna da mataimakin sa su ka rubuta sun mallaka, a lokacin da su ka fito takara, kafin su ci zaɓe.
Cikin wasiƙar da EFCC ta rubuta wa Shugaban CCB, Mohammed Isah, hukumar ta nemi ganin takardun bayyana yawan kadarorin da gwamnonin da mataimakan su su ka mallaka, domin hukumar ta ɗora bin-diddigi da binciken irin kadarorin da su ka tara lokacin da kowanen su ke kan mulki.
Wasiƙar EFCC Ga CCB:
“Hukumar EFCC na binciken mutanen da sunayen su ke cikin wannan wasiƙa.”
Haka EFCC ta aika wa CCB a ranar 11 Ga Afrilu, kuma wasiƙar ba Shugaban EFCC ne da kan sa, AbdulRashid Bawa ne ya sa mata hannu ba, ta na ɗauke da sa sa hannun Umma Sulaiman, Shugabar Sashen Binciken Maƙudan Kuɗaɗen Sata na EFCC.
EFCC ta nemi a ba ta kwafen yawan kadarorin gwamnonin da aka rantsar a 2015 da na waɗanda aka rantsar a 2019.
Sau da dama dai ana yawan zargin gwamnonin jihohi da laifin satar kuɗaɗen talakawan jihohin su, daga baya su sauka, su bar jihohin su a talauce, kuma a tsiyace. Kamar yadda wani binciken da ƙungiyar kare haƙƙin talakawa mai suna Transparency International ta tabbatar.
Bisa ga yin la’akari da ɗimbin kuɗaɗen da gwamnoni ke kashewa a lokutan zaɓe da kuma tafiyar da rayuwa ta ɓalle-bushasha da almubazzaranci, da yawan gwamnonin ana yi masu zargin ɗirka satar kuɗaɗen al’umma, saboda ko ta-soyu-gyaɗa ba su sayarwa su samu riba.
Wasu daga cikin tsoffin gwamnoni da ke fuskantar binciken EFCC sun haɗa da Godswill Akpabio, tsohon gwamnan Akwa Ibom da Abdul’aziz Yari, tsohon Gwamnan Jihar Zamfara. Su biyun su na nan shugabancin majalisar dattawa.
Cikin Maris, 2022 EFCC ta damƙe tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, a ranar da ya sauka mulki, a filin jirgin saman Legas, lokacin da ya yi ƙoƙarin arcewa Amurka.
Kafin shi an kama wasu da dama, an yi bincike, an gurfanar da wasu, wasu kuma har yau ba a san inda batun su ya kwana ba a hannun EFCC.
A yanzu EFCC na sa ido kan gwamnoni masu barin gado irin su Yahaya Bello na Kogi, da wasu tsoffin gwamnoni 11 da ba su kan mulki a yanzu.
Wasu na baya-bayan nan kuma sun haɗa da Bello Matawalle na Zamfara, wanda ake zargin cewa akwai Naira biliyan 70 a cikin ruwan cikin sa.
Sauran sun haɗa Nysome Wike na Ribas, Abdullahi Ganduje na Kano, Abubakar Bagudu na Kebbi, Abubakar Bello na Neja, Samuel Ortom na Benuwai, Ben Ayade, Dave Umahi, Okezie Ikpeazu, Ifeanyi Okowa, Nasir El-Rufai, Aminu Masari da Simon Lalong.
Akwai waɗanda a a yanzu sun samu damar komawa zango na biyu, wato Baka Mohammed na Bauchi da Ahmadu Fintiri na Adamawa.