Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sabbin nade-nade har guda 4 a Asusun Bunkasa Ayyukan Noma.
Nade-naden na kunshe ne a cikin wata sanarwa wanda kakakin fadar shugaban kasa ya fitar ranar Alhamis.
Buhari ya nada Garzali Abubakar, a matsayin babban sakataren Asusun bunkasa Ayyukan Noma (National Agricultural Development Fund).
Sauran wadanda aka nada sun hada da Aduke Hussain as Chairman, Hussaini Mohammed (Wakilin Arewa Ta Tsakiya ), Mohammed Umar (Wakilin Arewa Maso Yamma), Abdulsalam Ahmed (Wakilin Arewa Maso Gabas), Stella Uzokwe (Wakiliyar Kudu Maso Gabas), Stephen Ikata Wakilin Kudu Maso Kudu) da Olufunlayo Oluwole Faloye (Kudu Maso Yamma).
Wadannan nade-nade na daga cikin jerin ayuukan gaggawa da gwamnatin Buhari a cikin ‘yan kwanakin karshen mulkin ta.
Wani malamin Jami’ar Umaru Musa da ke Katsina ya ce irin wadannan nade-nade basu da amfani a lokacin da za a samu canjin gwamnati,
Abinda yafi dace wa shine, gwamnati maiu barin gado ta baiwa gwamnati mai zuwa shawara abinda ya dace a yi.
Discussion about this post