Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya bayyana cewa a duk shekara Gwamnatin Tarayya na kashe naira miliyan ɗaya kan kowane mutum ɗaya da ke tsare a gidajen kurkukun Najeriya.
Aregbesola ya ƙara da cewa hakan na nufin a wata ɗaya ana kashe wa kowane ɗan bursuna Naira 83,333.00 kenan.
Kakakin Yaɗa Labaran Minista Aregbesola, Sola Fasure ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar da yawun ministan, a ranar Asabar, a Abuja.
Aregbesola ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke ƙaddamar da Asibitin Kula da Masu Cutar Korona, wanda ake aikin ginawa a cikin kurkukun Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.
Asibitin mai cin gadajen kwantar da marasa lafiya 20, za a wadata shi ne da kayan aiki na zamani kuma masu inganci.
Aregbesola ya ce wannan muhimmin aikin gina asibiti ya ƙara tabbatar da ƙoƙarin da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi wajen inganta lafiya da rayuwar waɗanda ke tsare a gidajen kurkukun Najeriya daban-daban.
Ya ce inganta rayuwar ba a kan ɗaurarru kaɗai ta tsaya ba, har ma da ilahirin jami’an kula da gidajen kurkuku.
Ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya kawo kusan ƙarshen yadda ake fama da samun yawaitar ɗaurarru masu yawan kamuwa da cututtuka a gidajen kurkuku.
“A baya gidajen kurkuku sun kasance abin tsoro, ganin yadda ake yawan kamuwa da cututtuka daban-daban a ciki, musamman ma ƙazuwa, tarin fuka da sauran cututtukan da ke barazana ga lafiya da rayukan ɗaurarrun.
“Abin farin ciki ne a yanzu ganin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya magance wannan gagarimar matsalar da a yanzu kusan ta zama tarihi.
“A yanzu mu na da ingantattun asibitoci, magunguna da likitoci domin kula da ɗaurarru da kuma jami’an kula da gidajen kurkuku ɗin.
Sai dai kuma ya nuna damuwa kan ɗimbin kuɗaɗen da ake buƙata wajen samar da kayan inganta rayuwa, kayan aiki da kuma kuɗaɗen kula ko tafiyar da gidajen kurkuku na ayyukan yau da kullum.
Sai dai kuma ya ce tuni Gwamantin Tarayya ta magance wannan ƙalubalen.
“Kurkukun Fatakwal mai cin mutum 1,800, a halin yanzu mutum 3,067 ne cunkushe a cikin sa. Hakan ya nuna irin cinkoson da ake fama da shi a kowane gidan kurkuku na garuruwan faɗin ƙasar nan.” Inji Aregbesola.