Babab kotun Tarayya dake Akwa Ibom ta tsige Sufeto Janar din ‘yan sandan Najeriya daga ci gaba da nuna kansa da yin aiki a matsayin shugaban ‘yan sandan Najeriya.
Ko tu ta ce wa’adin baba ya cika tuntuni, dalilin haka ya sa ci gaba da zamansa a matsayin shugaban ‘yan sandan Najeriya ya haramta.
Da yake yanke hukuncin, Alkali Riman ya ce karin wa’adin da Buhari ya yi wa Sufeto Janar Baba ya saba wa tanadin dokar ‘yan sanda ta 2020.
“Yana da kyau a lura cewa Sufeto-Janar na ‘yan sanda ma’aikacin gwamnati ne kuma saboda kasancewarsa ma’aikacin rundunar ‘yan sandan Najeriya, sashi na 214 (1) na Kundin tsarin mulki da kuma abin da ya shafi Dokokin aiki na gwamnatin Tarayya mai lamba 299 (PSR) wanda ya tanadi yin ritayar dole na duk wani ma’aikacin gwamnati da ya kai shekaru 60 ko 35 yana aikin gwamnati duk sun tabbata akan sa.
Saboda haka duk da cewa wani gaba ce da shugaban kasa yayi amfani dashi wajen kjara masa wa’adi, saba wa doka ce a ci gaba da barin shi a wannan mukami na Sufeto janar din ‘yan sanda bayan wa’adin sa ya cika.
Discussion about this post