Kotun majistare dake Ikeja jihar Legas a ranar Laraba ta bada belin wata malamar makaranta Aderonke Makonde akan naira 50,000 bayan an kamata da laifin cin zarafin dalibar ta mai shekara 9.
Rundunar ‘yan sandan jihar sun Kai karan Makonde mai shekaru 35 kuma malamar makarantar Westgate Land Emperial dake Mushin bisa laifin lakadawa dalibar ta dukan tsiya.
Makonde ta musanta laifin da ake zargin ta da shi.
Dan sandan da ya shigar da karar Kehinde Ajayi ya ce Makode ta lakadawa dalibar dukan tsiya inda har ta ji wa yarinyar rauni a jikinta.
Ajayi ya ce malamar ta ce ta yi wa yarinyar wannan hukunci ne saboda ta kamata tana surutu a aji.
Alkalin kotun Mrs E. Kubeinje ta ce Makonde za ta gabatar da shaidu biyu da za su gabatar da shaidar suna biyan haraji wa gwamnatin jihar Legas da gabatar wa kotun da ingantacciyar adireshin wurin da suke zaune.
Za a ci gaba da shari’a ranar 7 ga Yuni.