Kotu a jihar Jigawa ta yanke wa tsohon Shugaban jami’yyar APC na jihar Habibi Sara hukunci daurin bisa zargin shirga kara da ya yi wa gwamnan jihar Muhammad Badaru.
Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ranar Alhamis bayan ‘yan sandan jihar sun kai kara gabanta bisa zargin kantara karya da yayi akan gwanan jihar a lokacinda yaki bakuntar wani shirin Rediyo a cikin watan Afirilu.
Sara ya yi ikirarin cewa gwamna Badarau tare da wasu manyan ‘yan siyasa sun zauna a kasar Saudiyya domin tattauna yadda za su yi wa gwamnatin zabebben gwamnan jihar Umar Namadu Zagon kasa.
“Gwamnan ya siya motoci domin raba wa kwamishinoni gwamnati mai jiran gado. Yin hakan bai kamata ba domin ba aikinsa bane ya siya motoci domin kwamishinoni sabuwar gwamnatin da za ta fara aiki.
“Shekaru 8 da suka gabata gwamna Badarau ya siya motoci 200 Wanda aka raba wa mutane a boye inda a yanzu muna bukatar bayanan yadda aka samu kudaden siyan motocin da wadanda aka raba wa motocin.
Sai dai kuma mataimakin gwamnan kan harkokin yada labarai Habibi Muhammad a wasikar shigar da kara ofishin ‘yan sanda da ya aika ya bukaci ‘yan sanda su kamo Sara da Wani mutum mai suna Karami Jahun wanda yake zargin yana yada labarin karya da kazafi akan gwamnan.
“Wannan maganar karya ce sannan an yi ta ne domin bata wa gwamnan da abokan aikinsa da ni a ciki suna. An Kuma Yi haka ne domin tada hankalin mutane da domin ganin an samu rashin jituwa tsakanin gwamna da gwamnati mai zuwa.
Alkali Balago ya yanke hukuncin daure Sara a gidan yari har sai ranar 8 ga Mayu domin ci gaba da shari’a.
Discussion about this post