Kotun Grade 1 dake Dei-Dei a Babban Birnin Tarayya Abuja ta yanke wa Rafiu Kosa mai shekaru 65 hukuncin share ofishin ‘yan sanda dake Zuba na tsawon mako guda bayan an kama shi yana kokarin yin sata.
Kotun ta yanke wa Kosa da shi makanike wannan hukunci bayan rundunar ‘yan sandan Abuja ta kai karar sa kotu bisa laifin kokarin yin sata da gararramba a gari.
Alkalin kotun Saminu Suleiman ya ce ya Yi la’akari da shekarun Kosa yayin da yake yanke hukunci da hakan ya sa ya bashi zabin biyan taran naira 2,000 ko Kuma ya share ofishin ‘yan sanda dake Zuba har na tsawon mako guda.
Suleiman ya ja kunnen Kosa da ya nisanta kansa daga aikata muggan aiyukka cewa idan har aka sake kama shi da aikata laifi orin haka kotu zata yanke masa hukunci mai tsauri.
Lauyan da ya shigar da karar Chinedu Ogada ya bayyana cewa a ranar 27 ga Afrilu ne Wani Divine Okoh ya kawo kara a ofishin ‘yan sanda dake Zuba.
Ogada ya ce Okoh ya fadi cewa ya ajiye motar sa a gefen titi, ya tsallaka ya yi bawali da ya juya kawai sai ya ga mutum ya afka C kin motan ya kokarin tada ita ya arce. Sai dai kuma Kosa bai iya arcewa da motar ba saboda dauki da mutanen wuri suka kawo masa.
Sai dai kuma Kosi ya ce ya yi kokarin arcewa da motar ne saboda bashin kudin gyaran moyar da yake bin shi mai motar.
“Ni dama na so na dauke motar na Kai na ajiye ta ne a ofishin ‘yan sanda dake Madalla amma sai ‘yan bangan dake Madalla suka kama ni.