Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaɓen shugaban kasa na watan Faburairu da aka gudanar a Najeriya, Peter Obi ya jaddada cewa ko tantam baya yi sai ya mulki ƴan Najeriya.
Da yake jawabi a wurin kaddamar da wani littafi mai taken (Peter Obi: Many voices, one perspective) a garin Awka jihar Anambra, Obi ya ce masu tunanin ba zai zama shugaban ƙasa ba a Najeriya, ruɗin kan su suke yi domin wannan fadar sai ya shige shi kuma ya mulki ƴan Najeriya.
” Ma su ganin ai ba zan zama shugaban kasa ba, su sani daga yau cewa mafarki suke yi amma mulkin Najeriya kamar na yi shi na gama ne. Dole in zama shugaban Najeriya ko ana so ko ba a so, ko yau ko kuma gobe amma tabbas zan shugabanci kasar nan.
“Wadanda suke son zama shugaban kasa a Najeriya ya zo su gaya mana abinda suka yi a baya, da abinda za su yi.
” Bani da takardar zama ɗan wata kasa banda Najeriya, ita kenan mun kuma babu inda zan tafi ina nan a nan. Sannan ina so in sanar muku cewa ko a lokacin da na tafi kotu ina kalubalantar zaɓen gwamna na a Anambra, da yawa wasu na cewa bata lokaci na nake yi.
” Amma duk da haka ban karaya ba na lashi tabobin sai naga abinda ya ture wa buzu naɗi ko da ko shekaru 4 kaf za a yi a na shari’a. Daga karshe sai gashi na yi nasara.