A wasikar wanda PREMIUM TIMES ta cinkaro da ita, iyalan tsohon gwamnan Ahmed Makarfi na rokon gwamnatin El-Rufai ya yi musu sassauci kada ya kwace filayen nan wanda mallakin kamfanin Canes ne karkashin Makarfi.
A cikin wasikar, iyalan Makarfi na rokon gwamnatin Kaduna ta kara musu lokaci su gina waɗannan filaye da wasun su ma sun fara aiki a a kan su.
A cikin duka Wasiƙun da ke dauke da sa hannun babban manajan Kamfanin Canes, Ibrahim Ahmed Makarfi, sun bada bayanan yadda yanayin filayen suka.
Filaye ne har guda tara wanda ke karkashin mallakin iyalan tsohon gwamnan. Daya daga cikin filin shine wani katafaren fili dake Magadisu. Sai dai kuma tuni gwamnati ta mika filin ga Sahad, wanda tuni har ta kammala gina shi.
Sai kuma wasu filayen dake Kwato road, wanda suma duk an fara aiki a cikin su amma kuma ba a gama su ba.
A cikin wasikar wanda suke rokon gwamnatin El-Rufai kada ta kwace su, ta dawo wa iyalan filayen sun bayyana cewa ba da gangar suka ki gine filayen ba.
Sun ce akwai matsala daga hukumar raya birane na jihar Kaduna wanda bata kammala bata damar ci gaba da aiki a wasu filayen ba sannan kuma da wasu matsaloli da ya saha kan su. Amma kuma sun roki gwamnati ta yi hakuri da kara masu lokaci domin kammala aikin da suka fara akan wadannan filaye.
PREMIUM TIMES ta yi kokarin ji daga bakin wani jami’in gwamnati. Kaduna amma abin ya citura.
Daga karshe dai wani jami’in gwamnati da ya roka a sakaye sunansa saboda ba a bashi damar yin magana a kai ba ya shaida mana cewa tun a shekarar 2018 gwamnati take kwankwasa wa Makarfi kofa kan waɗannan filaye da gine-ginen da ya ki kammala wa kuma ko a lokacin irin kukan da su ka yi kenan na a basu karin lokaci su gina, lokacin ne har yanzu babu abinda aka yi a kai.
Discussion about this post