Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta ya aika wa Majalisar Dokokin Delta ƙwarya-ƙwaryan kasafin naira biliyan 71.
Maƙudan kuɗaɗen waɗanda idan majalisar jihar ta amince, za a kashe su ne cikin kwanaki 14 ɗin da su ka rage wa Gwamna Okowa kan mulki.
Ya ce za a kashe kuɗaɗen wajen biyan ayyukan da a yanzu haka ake kan yi a faɗin jihar.
Mataimakin Kakakin Majalisar Jihar Delta, Christopher Ochor ne ya karanto wasiƙar neman amincewa da kasafin.
Okowa ya shaida masu cewa za a kashe naira biliyan 5.6 wajen gudanar da ayyukan yau da kullum, sai kuma Naira biliyan 65.5 kuma za a biya ‘yan kwangila ne kuɗaɗen manyan ayyukan raya ƙasa waɗanda ba a biya su ba.
“A kan haka na ke neman alfarmar majalisa ta sa hannun amincewa a yi kasafin, domin a yi wasu ayyuka na gwamnati, a biya ‘yan kwangilar da ke kan gudanar da manyan ayyukan raya jiha.”
Shugaban Masu Rinjaye, Ferguson Onwo ya gabatar da kasafin, kuma har an yi masa karatun farko.
Gwamna Okowa dai shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Atiku Abubakar a zaɓen 2023.