Wani ɓangare daga cikin gungun Zaɓaɓɓun ‘Yan Majalisar Tarayya ya ɓalle, ya nuna goyon bayan sa ga Tajuddeen Abbas da Ben Kalu, waɗanda APC da Tinubu ke so su zama Kakaki da Mataikakin Kakakin Majalisar Tarayya.
Hakan ya nuna cewa an samu babuwar kawuna kenan a zaɓaɓɓun ‘yan majalisar, kamar yadda aka sanar a cikin wata sanarwar bayan taro, a ranar Litinin, bayan tashin su daga wani taro a otal ɗin Hilton, a Abuja.
Ige Igariwey ɗan PDP daga Ebonyi da Alhassan Rurum, ɗan NNPP daga Kano, su ne su ka rattaba hannayen su a kan takarar sanarwar bayan tashi daga taron.
“Bayan mun yi dogon nazari da hangen nesa, mu dai mun yanke shawarar cewa mu na goyon bayan Tajuddeen Abbas da Ben Kalu, a matsayin Kakakin Majalisar Tarayya da Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya.
“Mun auna cewa za a samu kyakkyawan shugabanci a hannun Abbas da Ben Kalu a majalisa.
“Nan gaba kuma za mu yi babban taron da zai ƙara haɗawa da sauran mambobin jam’iyyun adawa masu yawa, domin mu ƙarƙare fito da matsayar mu ta goyon bayan Abbas da Ben Kalu a fili.
Makonni biyu da suka gabata, wannan jarida ta buga labarin yadda zaɓaɓɓun gamayyar jam’iyyun adawa sun kafa kwamitin fito da ɗan takara ɗaya tilo.
Zaɓaɓɓun ‘yan majalisar tarayya daga jam’iyyun adawa bakwai sun fitar da sanarwar cewa za su yi amfani da yawan su a jimlace domin su samar da shugabannin Majalisar Wakilai ta Ƙasa.
Jam’iyyun sun haɗa da PDP, LP, NNPP, APGA, SDP, ADC da YPP.
A cikin watan Yuni ne dai za a ƙaddamar da Zauren Majalisar Dattawa da ta Wakilai ta Ƙasa.
Sun cimma wannan matsaya ce a cikin wata sanarwa da Dachung Bagos na PDP daga Jihar Filato da kuma Afam Ogene na LP daga Jihar Anambra da Gaza Gbefwe, ɗan SDP daga Nassarawa, ya ce za su cure su 188 domin su kayar da duk wani ɗan takarar da APC mai rinjaye za ta tsayar.
Ya ce APC su 177 ne, su kuma gamayyar mambobin adawa su 183 ne.
Tuni dai su ka kafa kwamitin mambobi 13 ƙarƙashin shugabancin Nicholas Mutu, ɗan PDP daga jihar Delta a matsayin shugaban kwamiti.
Wani rikicin kuma ya ƙara kunno kai a cikin wakilan APC, yayin da Wase, Betara, Doguwa, Soli da Jaji sun ƙi yin mubaya’a ga Abbas, wanda Tinubu da APC ke ƙauna.
Manyan da ke sahun gaba a Majalisar Tarayya, kuma masu takarar shugabancin majalisar, sun ce ba su amince da wanda Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu da APC ke so ya zama Kakakin Majalisar Tarayya ba.
Tinubu da APC dai sun nuna goyon bayan su ga Tajuddeen Abbas daga Kaduna da kuma Ben Kalu daga Abiya.
Sai dai kuma Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya Idris Wase, Tijjani Betara, Barau Jibrin, Sada Soji da Jaji duk sun ki amincewa da tsarin da Tinubu da APC su ka fito da shi.
Wase ne ya bayyana wannan matsaya ta su a ranar Litinin a otal ɗin Hilton, wurin ƙaddamar da takarar Muktar Betara, a Abuja.
Wase ya ce su biyar ɗin su yanke shawarar tafiya tare cikin haɗin kai domin su yi fatali da zaɓin da Tinubu da APC su ka yi.
Sauran inji shi sun haɗa Sada Soli, Alhassan Doguwa, Ahmed Jaji da Muktar Betara.
Betara dai ya fito jihar Borno, inda Zaɓaɓɓen Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya fito.
Shi kuma Doguwa, ya na fuskantar tuhuma a kotu, bisa zargin kisan ‘yan adawa lokacin zaɓen majalisar tarayya a mazaɓar sa ta Doguwa/Tudun Wada, Kano.
A wurin taron ƙaddamar da Betara, cincirindon ‘yan majalisar da ke wurin sun riƙa fitowa fili su na nuna goyon bayan su ga waɗannan biyar ɗin, tare da nuna rashin goyon bayan Tajuddeen Abbas wanda Tinubu da APC ke so.
Yusuf Gagdi da Miriam Onuoha su ma sun halarci taron, amma dai su ba su fito sun ƙalubalanci Tinubu da APC ba.
Wase ya ce bai goyi bayan duk wata matsayar da su Tinubu da APC su ka ɗauka ba tare da tuntuɓar majalisa ba.