Ɗan Majalisar Tarayya wanda kuma ke sahun gaba na masu adawa kan batun fito da Kakakin Majalisar Tarayya, Yusuf Gagdi, ya bayyana cewa rashin adalci ne tantagarya da APC ta bayar da shugabancin majalisar tarayya ga jihar Kaduna.
Gagdi ya ce Jihar Kaduna ba ta tsinana wa APC komai ba a zaɓen shugaban ƙasa.
Ya ce wannan rashin adalci da APC ta yi, ya zubar mata da ƙimar da ba ta za iya tirsasa mambobin majalisa su bi tsarin da jam’iyya ke so a bi ba wajen fitar da shugabannin majalisa.
Gagdi dai ya na wakiltar ƙananan hukumomin Pankshin/Kanam da Kanke.
Ya bayyana haka a ranar Litinin lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a otal ɗin Hilton, ranar Talata, a Abuja.
“Don me aka zaɓe ni a Majalisar Tarayya ne? Ai an zaɓe ni ne don na yi wa ƙasa ta wakilci, kuma na tabbatar an yi wa kowa adalci. Ton ba zan bari jam’iyyar da aka zaɓe ni a ƙarƙashin ta kuma ta fito za ta yi rashin adalci, sannan ku yi tunanin na amince da rashin adalcin na ta.
“Na yi nazarin lamarin nan fa. Kuma na yi maku bayani ƙarara, ko makaho da kurma da bebe duk sun yarda cewa an yi rashin adalci. Amma wai ana ta batun hukuncin da jam’iyya ta yanke ba mai tayar da shi.”
APC Ta Yi Wa Yankin Mu Sakayyar Ƙoƙarin Mu Lokacin Zaɓe Mana:
Da ya ke magana dangane da bai wa Kaduna alfarmar fito da Tajuddeen Abbas ya zama Kakakin Majalisar Tarayya, Gagdi cewa ya yi idan aka yi la’akari da yawan ƙuri’un da APC ta samu a jihar Kaduna lokacin zaɓen shugaban ƙasa bai kai yawan da za a yi mata sakayya da shugabancin majalisar tarayya ba.
Ya ce Ƙaramar Hukuma ɗaya tal APC ta yi nasara a zaɓen Shugaban Ƙasa a Jihar Kaduna. Don haka rashin adalci ne a bai wa Kaduna Kakakin Majalisar Tarayya sukutum, shi kuma yankin Arewa ta Tsakiya da ya haɗa da Filato, Benuwai, Nasarawa, Kogi, FCT Abuja da Neja su tashi a tutar babu.
“Shi dai Bola Tinubu ya ce zai yi wa yankunan da su ka yi biyayya da kyakkyawar sakayya. To a jihar Kaduna dai Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari kaɗai APC ta ci. To don me za a bai wa Kaduna Kakakin Majalisar Tarayya?” Inji Gagdi.