Duk da kurin da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai na tarayya Ado Doguwa ya rika yi cewa babu wanda aya isa ya sa shi ya janye daga takarar kakakin majalisar tarayya, ya janye daga takarar.
Doguwa ya bayyana cewa ” Ni mutum mai ɗa’a da kishin jam’iyya. Tunda abinda jam’iyya take so kenan wato Tajuddeen Abbas ya zama kakakin majalisa nima na bi daga yau.
Wannan shawara da Doguwa ya yanke ya biyo bayan ganawa ne da akbda shi da wasu ƴan jam’iyyar da ke kokarin daidata tsakanin ƴan majalisan su dawo su bi zaɓin jam’iyyar wato Tajuddeen Abbas, ya zama kakakin majalisar tarayya.
Bayan Doguwa wasu ƴan takara biyu suma sun janye wa Abbas.
Ƴan takaran sune, Abubakar Makki (APC, Jigawa) ds Tunji Raheem (APC, Kwara).
Sai dai kuma har yanzu gaggan masu neman kakakin majalisar tarayya wato Mukhtar Betara da Idris Wase har yanzu sun kafe akan bakan su na kin janye wa Tajuddeen Abbas.
Discussion about this post