A kotun shari’a dake jihar Kaduna ne Fatima Aliyu mai shekaru 20 ta kai karar mahaifinta Aliyu Muhammad dalilin kokarin yi mata auren dole da wanda bata so.
Fatima wacce ke magana ta bakin lauyanta dake kare ta Malam Y.A Bulama ta ce mahaifinta ya na matsamata lallai sai ta auri wani wadda ba ta so dole bayan ga wanda take so.
Bulama ya ce Fatima ta maka mahaifinta a kotu ne ba don ta nuna masa rashin kunya ba ko kuma wani abu makamancin haka, sai don a kwato mata hakkin ta don bata son shi.
Shi kuwa Muhammad ya ce tun mahaifan sa na da rai ne suke yi musu baiko cewa za su auri juna. Dalilin haka ne ya sa ya ke so ya ga ya cika burin iyayen na su.
“Na aurar da ‘ya’ya na mata shida a kauyen nan kuma duk sana zaman lafiya da mazajen su.Ina tabbatar muku cewa mahaifiyar Fatima ce ke zuga ta ta bijire wa wannan abin alheri da nake so na kulla.
Alkalin kotun Malam Isiyaku Abdulrahman ya ce bisa ga dokan shari’a Muhammad na da ikon zaba wa ‘yarsa mijin aure.
Sai dai kuma Abdulrahman ya ce bai kamata a yi mata auren dole ba.
A karshe dai alkalin kotun ya hore su duk biyun su yi abinda ya dace. kadsa a yiwa fatima Auren dole ita kuma ta bi umarnin mahaifanta shine ya fi dacewa.
Discussion about this post