Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi wa ‘yan Najeriya alƙawarin cewa zai taka muhimmiyar rawa wajen haɓbaka Najeriya da ‘yan ƙasar fiye ma da yadda ake tsammani.
Ya ce zai magance dukkan matsalolin da su ka dabaibaye ƙasar.
Tinubu ya yi wannan alƙawarin ne a ranar Lahadi, kwana ɗaya kafin a rantsar da shi.
Da ya ke jawabin da Babban Ɗakin Taro na Fadar Shugaban Ƙasa, a Abuja, Asiwaju ya ce ƙuncin rayuwa, fatara da talauci na daga cikin abubuwan da ke addabar ƙasar nan.
Ya sha alwashin cewa babu wani dalilin da gwamnatin sa za ta kawo ta ce shi ne ya hana ta magance ƙalubalen da ke damun ƙasar nan.
“Zuwa gobe wanda zan gaji mulki a hannun sa zai tafi Daura kan iyaka da Nijar. Amma na ce masa kada ya samu damuwa. Zai riƙa zuwa sai dai ya ji ina ƙwanƙwasa mana ƙofa.
“Komai gajartar mutum zai iya hangen sararin samaniya. Duk lokacin da na ke neman taimakon sa, zan je duk inda ya ke na same shi.” Inji Tinubu.
Ya ce Najeriya ƙasa mai cike da al’ummar da ke da juriya. Ta sha yin tuntuɓe, amma ba ta yarda ta kai ƙasa.
‘Yan Najeriya kamar tsohuwar mota ce mai nagarta, ba za ta taɓa lalacewa a kan hanyar tafiya ba.
“Tilas mu yi yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran matsalolin da su ka addabi aikin gwamnati.
“Amma kada ma ku je tausayi na. Ni na nemi mulki, na yi yawon kamfen, don haka ba ni da wani uzirin da zan ce maku shi ya hana ni cika alƙawurran da na ɗauka.”
Idan za a tuna, a jawabin bankwana da Buhari ya yi, ya ce ‘Tinubu yau mafarkin ka ya zama gaskiya, Allah ya sa ka kai Najeriya fiye da inda na kai ta’.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu cewa ya gode wa Allah, tunda mafarkin da ya daɗe ya na yi, yanzu ya tabbata.
A cikin jawabin bankwana da Shugaba Mai Barin Gado Buhari ya yi a ranar Lahadi da safe, ya roƙi Tinubu tare da yi masa addu’a da fatan ya haɓɓaka Najeriya, tare da ciyar da ita gaba, fiye da inda shi Buhari ya kai ƙasar daga 2015 zuwa 2023.
Buhari ya ce duk a cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa wanda Tinubu ya yi takara da su, shi ne mafi cancanta.
Dangane da haka ne ma Buhari ya ce ba a taɓa gwagwagwar zaɓen shugaban ƙasa kamar na 2023 ba.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tun Jamhuriya ta Farko zuwa yanzu ba a yi zaɓen shugaban ƙasa wanda aka yi gwagwagwa kamar na 2023 ba.
Ya ce ya na farin ciki ganin wannan ne zaɓen da ya zo daidai ƙarshen wa’adin sa, kuma ya karɓi mulki a hannun farar hula, shi ma zai bayar da mulki ga farar hula, gwamnatin da jama’a su ka zaɓi abin su da kan su.
Shugaba mai barin gado Buhari, ya yi waɗannan kalamai a cikin jawabin sa na ban-kwana ga ‘yan Najeriya, wanda ya gabatar ranar Lahadi da safe.
Ya ce don haka ya zama tilas a ci gaba da ganin cewa dimokraɗiyya ta ɗore, kuma an ƙara inganta tsarin zaɓe, domin shi ne ƙashin bayan nagartacciyar dimokraɗiyya.
Wannan dimokraɗiyya ta na da kwarjini, nagarta da kuma armashi, domin ta bayar da dama duk wanda ya ke ganin an yi masa rashin adalci, zai iya matsawa gaba ya ɗaukaka ƙara, kotu ta karɓar masa haƙƙin sa.
“Saboda haka ina roƙon da wanda ya kai ƙara da wanda aka kai, su riƙa yin tawakkali su na karɓar hukuncin kotu da zuciya ɗaya. Domin ta haka ne za a gina ƙasaitacciyar Najeriya.”
Shugaba Buhari ya jinjina wa dukkan ‘yan takarar shugaban ƙasa a zaɓe, tare da cewa sun cancanci yabo ganin yadda su ka yi amanna da tsarin kotunan mu, har su ka garzaya kotu, bisa yaƙinin cewa za su yarda da sakamakon hukuncin da kotu za ta yanke.
“Ina taya aboki na na tsawon lokaci, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bisa samun nasarar da ya yi har ya cika burin sa rayuwa. Hakan kuwa ya tabbata ne saboda juriyar da ya daɗe ya na nunawa wajen gwagwagwar kishin Najeriya.”
Discussion about this post