• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Minista Sadiya ta miƙa ragamar Ma’aikatar Harkokin Jinƙai ga Babban Sakatare

    2015-2023: ‘Na yi sukuwa ta lafiya, na kai zamiya lafiya’ – Buhari

    BANKWANA DA BUHARI: ‘Tinubu yau mafarkin ka ya zama gaskiya, Allah ya sa ka kai Najeriya fiye da inda na kai ta’ – Nasihar Buhari ga Asiwaju

    Tsakanin Sanata Barau da Gwamna Ganduje, Daga Jaafar Jaafar

    Ba zan jira Litinin ba, tun Lahadi zan mika mulki ga Abba Gida-Gida in kama gaba na – Ganduje

    RANTSAR DA TINUBU: Kotun Koli ta yi watsi da karar rashin cancantar Tinubu shiga zaɓen 2023

    RANAR RANTSAR DA TINUBU: Za mu hana makiyaya karakaina da shanu a cikin Abuja – Shugaban Miyetti Allah

    An Karrama gidan Jaridar PREMIUM TIMES da kyauta mafi daukaka a aikin Jarida na kasar Amurka

    BA DA MU BA, TAYA ƁERA ƁARI: PREMIUM TIMES ta nesanta kan ta daga ƙungiyar da ta jona sunan ta a shirya taron karrama wasu mutane

    KIRAN RUWA: ‘Ka wa Allah ka ɗaga mana kafa, kada ka kwace mana filayen mu har 9 da ka kunno kai a kan su – Makarfi ga El-Rufai

    ‘Ni da Wike kaman ‘Yan biyu ne, muna tsage gaskiya komai dacin ta’ – El-Rufai

    SABODA TIWITA: Sanatocin PDP sun fice daga Zauren Majalisar Dattawa

    Zaɓaɓɓun Sanatocin Arewa ta Tsakiya sun nemi a ba su Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ko a-yi-ta-ta-ƙare

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

No Result
View All Result

JAYAYYAR NASARAR TINUBU: Shin ta yaya za a riƙa shari’ar ƙarar Atiku, Peter Obi da APM, bayan kotu ta dunƙule su wuri ɗaya?

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
May 25, 2023
in Rahotanni
0
JAYAYYAR NASARAR TINUBU: Shin ta yaya za a riƙa shari’ar ƙarar Atiku, Peter Obi da APM, bayan kotu ta dunƙule su wuri ɗaya?

Babban dalilin da Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta bayar na dunƙule ƙararrakin zaɓen da Atiku Abubakar, Peter Obi da APM su ka shigar kan Bola Tinubu, shi ne saboda rashin isasshen lokacin da za a iya shafe watanni ana shari’un.

Ita dai doka kwanaki 180 ta bayar daga ranar shigar da ƙara cikin Maris zuwa cikin Satumba da za a yanke hukunci. Daga nan kuma wanda bai gamsu ba, sai ya zarce Kotun Ƙoli. A Kotun Ƙoli ma za a kammala shari’un ne a cikin Disamba.

A ranar Talata ce dai kotun ta dunƙule shari’un uku wuri ɗaya. Abin da ya rage yanzu shi ne a ga yadda za a yi zaman shari’un ya inda su ka yi kamanceceniya da juna da kuma inda su ka bambanta.

Atiku Da Peter Obi:

Su biyu dai kowanen ya na iƙirarin cewa shi ne ya yi nasara, ba Bola Tinubu wanda INEC ta ayyana ba.

Sun yi zargin an tafka maguɗi sosai a faɗin ƙasar nan a jihohi daban-daban.

Kowanen su a cikin su biyu na so a bayyana shi a matsayin shi ne halastaccen wanda ya yi nasara a zaɓen, ba Tinubu ba.

Haka kuma su na tantamar cewa lallai Tinubu bai cancanci tsayawa takarar zaɓe ba.

Wani gurbin da Atiku da Obi su ka haɗu kuma shi ne sun shaida wa kotu an baddala sakamakon zaɓe a jihohi 12, kuma Tinubu bai samu kashi 25 ba a zaɓen shugaban ƙasa a Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja ba.

Sai kuma ɓangarorin biyu kowa ya shigar da ƙara cewa idan ba a ba shi nasara ba, to a soke zaɓen, a sake wani sabon zaɓe.

Matsayar Jam’iyyar APM:

A ƙarar da ta shigar, APM ta ce Tinubu bai cancanci shiga takarar zaɓe ba, ballantana har ya ci zaɓen.

Saboda haka sai APM ta nemi a soke nasarar Tinubu, tunda bai cancanci shiga zaɓe ba, a bai wa Atiku Abubakar, wanda ya zo na biyu.

Na biyu kuma APM ta ce nasarar Tinubu haramtacciya ce, domin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya raba ƙafa a shiga takara.

APM ta ce lokacin da aka ɗauki Shettima takarar mataimakin shugaban ƙasa, can a jihar Borno kuma ya fito takarar sanata. Hakan inji APM keta dokar zaɓe ce.

Saboda haka APM na neman kotu ta kori Tinubu da Shettima nasarar zaɓen 2023.

Ta Yaya Kotu Za Ta Saurare Su?

Wannan ne karon farko a tarihin shari’un zaɓe a Najeriya da aka dunƙule ƙararrakin zaɓe wuri ɗaya.

Wasu ƙwararrun lauyoyi na ganin cewa kowane mai ƙara zai shigar da ta sa ne, kuma ya kirayi shaidun sa daban. Amma a ƙarshe sai kotu ta yanke hukunci ɗaya tal, a lokaci ɗaya, kuma a rana ɗaya.

An dai yi daidaito cewa su ukun sun kai ƙarar yawan adadin da kowane ya shigar a kotu, wato duk wanda Atiku ya maka kotu, su ne dai Obi da APM su ka maka kotu.

Wato kowanen su ya kai ƙarar INEC, Tinubu da APC. Amma ita APM sai ta ƙara da Kashim Shettima.

Yadda Kotu Ta Dunƙule Ƙararrakin Atiku, Peter Obi Da APM Wuri Ɗaya:

Wannan jarida dai a ranar Talata ta buga labarin yadda kotu ta dunƙule ƙarrarakin Atiku, Peter Obi da ta APM wuri ɗaya.

Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Ƙasa da ke zama a Abuja, ta dunƙule ƙarar da Peter Obi da Atiku Abubakar da jam’iyyar APM su ka shigar a wuri ɗaya.

Su ukun su na ƙalubalantar nasarar da INEC ta ce Bola Tinubu na jam’iyyar APC ya yi a zaɓen shugaban ƙasa a ranar 25 ga Fabrairu.

Yayin da Atiku da Obi kowa ke neman a ƙwace daga hannun Tinubu a ba shi, ko kuma a sake zaɓe baki ɗaya, ita kuwa jam’iyyar Allied Peoples’ Movement, wato APM ta na so kotu ta ƙwace ne daga hannun Tinubu ta bai wa Atiku wanda ya zo na biyu. Ta na zargin cewa Tinubu bai cancanci tsayawa takarar shugaban ƙasa ba.

Alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa su biyar ƙarƙashin Haruna Tsammani, sun dunƙule ƙararrakin uku wuri ɗaya, kamar yadda PDP ta nemi a yi a ranar Litinin.

Tsammani ya ce ya yi amfani da Saɗara ta 50 ta Sabuwar Dokar Zaɓe ta 2022, aka dunƙule ƙararrakin uku wuri ɗaya.

Ya ce idan an yi hakan, an yi wa shari’a adalci kenan.

Kotu ta tuna masu cewa daga tsakiyar Maris dai kwanaki 180 doka ta bayar a kammala shari’un gaba ɗaya.

A kan haka kotu ta umarci Peter Obi ya kammala gabatar da ba’asin sa da hujjoji da shaidu a cikin makonni uku, maimakon makonni shida da lauyoyin sa su ka ɗiba da farko.

Saboda haka kotu a ranar Talata ta ce wa babban lauyan Obi wato Livy Uzoukwu zai fara bayanan hujjoji da gabatar da shaidu daga ranar 30 Ga Mayu zuwa 23 Ga Yuni. Kuma za a riƙa zaman sauraren ƙararrakin daga Litinin har zuwa ranakun Asabar.

Peter Obi ya kai ƙarar Tinubu, APC, INEC da Kashim Shettima. Don haka sai kotu ta ba su huɗun kowanen su kwanaki biyar-biyar su kare kan su.

A ranar Litinin ce dai lauyoyin Atiku, Peter Obi da APM su ka nemi kotu iznin dunƙule ƙarar su wuri ɗaya, amma Tinubu da APC su ka ƙi yarda.

Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, shi da APC sun roƙi Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓe kada ta amince da roƙon da Atiku, Obi da jam’iyyar APM su ka yi, na neman iznin su dunƙule ƙarar su wuri ɗaya, maimakon a riƙa sauraren kowane daban-daban.

Atiku da Obi da APM duk su na ƙalubalantar nasarar da INEC ta ce Tinubu ya yi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Yayin da Atiku da Obi kowa ke neman ko dai a ba shi nasara, ko kuma a soke zaɓen a sake sabo, ita kuwa jam’iyyar APM ta shigar da ƙara cewa Tinubu bai ma cancanci tsayawa takara ba, don haka a soke zaɓen sa, a bai wa Atiku Abubakar wanda ya zo na biyu nasara kawai.

Lauyan Tinubu mai suna Akin Olujinmi, wanda tsohon Antoni Janar na Tarayya ne, ya roƙi Alƙalai biyar masu shari’ar bisa jagorancin Haruna Tsammani cewa kada su bai wa su Atiku iznin dunƙule ƙararrakin na su wuri ɗaya. Ya ce idan aka yi haka, to an yi wa shari’a ita kan rashin adalci.

Duk da Olujinmi ya yarda cewa wasu ƙararrakin na su Atiku, Obi da APM iri ɗaya ne, ya ce ai kuma akwai inda su ka sha bamban.

A zaman da kotun ta yi na ranar Asabar dai, wannan jarida ta ruwaito cewa APC za ta gabatar da shaidu 25, Tinubu shaidu 39.

A ƙoƙarin ta na ganin Atiku Abubakar, ɗan takarar PDP a zaɓen 2023 bai ƙwace nasara daga hannun Bola Tinubu ba, Jam’iyyar APC za ta gabatar wa Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa shaidu har guda 25.

A na sa ɓangaren, Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai gabatar da shaidu 39.

Babban Lauyan APC za shari’ar mai suna Solomon Jimoh shi ne ya bayyana wa kotun haka a ranar Asabar a zaman ta na ƙarshen mako. Ya ce zai gabatar da shaidu 25.

A ranar Litinin ce 22 ga Mayu za a ci gaba da zama, kamar yadda Shugaban Alƙalan Kotu su biyar, Haruna Tsammani ya yi sanarwa.

Atiku dai a ta bakin lauyan sa, ya shaida wa kotu cewa zai gabatar da shaidu 100, domin taya shi kai ƙeyar Asiwaju ƙasa.

Makonni biyu kafin a rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu, a Kotun Ɗaukaka Ƙarar Zaɓen Shugaban Ƙasa kuma shari’a ta fara zafi yayin da aka kai matakin fara sauraren shaidun da za a fara gabatarwa a kotu.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, zai bijiro wa kotu da shaidu guda 100, domin ya tabbatar wa kotu zargin maguɗin da ya ke iƙirarin cewa an yi a zaɓen 25 ga Fabrairu, 2023.

A ɗaya ɓangaren kuwa, lauyoyin Tinubu sun bayyana wa kotu cewa za su gabatar da shaidu 39 domin kare zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da kujerar sa.

A ranar Asabar ce lauyoyin ɓangarorin biyu su ka gabatar wa Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa wannan aniya ko shiri da kowane ɓangaren ke yi.

Sauraren shari’un dai za su shiga surƙuƙin hayaƙi, bayan an shafe makonni biyu ana ban-tafin-hannun-makahon Turanci tsakanin lauyoyin a kotu.

Ana sa ran za a shafe watanni ana tafka shari’a har bayan rantsar da Tinubu kan mulki.

Ba za a kulle ƙofar shari’a ha har sai cikin Disamba, domin duk ɓangaren da bai gamsu da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙarar Zaɓen Shugaban Ƙasa ba, ya na da damar wucewa Kotun Ƙoli.

Atiku ya na ƙalubalantar INEC cewa ba ta bi ƙaidojin da dokar ƙasa ta shimfiɗa ba kafin ta ayyana cewa Bola Tinubu ne ya yi nasara.

Haka shi ma Peter Obi na LP da ita jam’iyyar LP ɗin, sun shigar da kusan irin ƙara ɗaya da wadda Atiku da PDP su ka shigar.

A ranar Asabar, Babban Lauyan Atiku mai suna Chris Uche, ya bayyana adadin yawan shaidun da ɓangarorin lauyoyin biyu su ka amince za su gabatar wa kotu.

Sannan kuma sun amince da irin tsarin gabatar da kwafe-kwafen takardun hujjoji da za a riƙa gabatarwa.

“Mun yi shirin gabatar da shaidu har mutum 100. Za mu shafe makonni uku kaɗai mu na gabatar da shaidun mu ɗaya bayan ɗaya, maimakon makonni bakwai da aka ɗibar mana na ƙa’idar lokaci.” Inji Uche, babban lauyan Atiku.

“Ɓangarorin biyu sun amince cewa kowane mai shaida na mai ƙara da na mai kare kan sa, za a ba shi minti 30 ya yi magana a kotu.

“Sai lauyan wanda ake karewa kuma za a ba shi minti 15 ya yi masa tambayoyi. Sai kuma ƙarin minti biyar na ƙarƙare tambayoyin da ka iya biyo baya.”

Tinubu Zai Gabatar Da Shaidu 39:

Lauyan Tinubu mai suna Roland Otaru, ya shaida wa kotu cewa za su gabatar da shaidu 39 a matsayin shaidun kare nasarar Tinubu.

Otaru ya ce jagoran lauyoyin Tinubu, Wole Olanipekun zai buƙaci kwanaki 9 domin ya gabatar da shaidun na su.

“Sun kuma amince cewa ɓangaren da zai gabatar da kwafe-kwafen takardun shaida a kotu, zai aika wa ɗaya ɓangaren da kwafen su ma aƙalla sa’o’i 48 kafin zaman kotu.”

Sai dai lauyan Tinubu ya ce shaidun da za su riƙa gabatarwa kowane zai riƙa yin minti 20 ya na bayani a kotu, ba minti 30 kamar na shaidun Atiku ba.

Tags: AbujaAPCbiHausaNewsPREMIUM TIMESTinubu
Previous Post

CBN ya ƙara tsula kuɗin ruwa zuwa kashi 18.5% bisa 100%

Next Post

RANAR RANTSAR DA TINUBU: Za mu hana makiyaya karakaina da shanu a cikin Abuja – Shugaban Miyetti Allah

Ashafa Murnai

RANAR RANTSAR DA TINUBU: Za mu hana makiyaya karakaina da shanu a cikin Abuja - Shugaban Miyetti Allah

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Ganduje ya bar wa Kano bashin Naira biliyan 241, Abba ya ce zai bi ya gano hanyoyin da aka ciwo bashin
  • Minista Sadiya ta miƙa ragamar Ma’aikatar Harkokin Jinƙai ga Babban Sakatare
  • JAWABIN BANKWANA: Ba a taɓa gwagwagwar zaɓen shugaban ƙasa kamar na 2023 ba – Buhari
  • JIGAWA A HANNUN BADARU: Yadda shekaru takwas na mulkin APC ya kasa rage katutun talauci da fatara
  • BANKWANA DA BUHARI: ‘Tinubu yau mafarkin ka ya zama gaskiya, Allah ya sa ka kai Najeriya fiye da inda na kai ta’ – Nasihar Buhari ga Asiwaju

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.