Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tun Jamhuriya ta Farko zuwa yanzu ba a yi zaɓen shugaban ƙasa wanda aka yi gwagwagwa kamar na 2023 ba.
Ya ce ya na farin ciki ganin wannan ne zaɓen da ya zo daidai ƙarshen wa’adin sa, kuma ya karɓi mulki a hannun farar hula, shi ma zai bayar da mulki ga farar hula, gwamnatin da jama’a su ka zaɓi abin su da kan su.
Shugaba mai barin gado Buhari, ya yi waɗannan kalamai a cikin jawabin sa na ban-kwana ga ‘yan Najeriya, wanda ya gabatar ranar Lahadi da safe.
Ya ce don haka ya zama tilas a ci gaba da ganin cewa dimokraɗiyya ta ɗore, kuma an ƙara inganta tsarin zaɓe, domin shi ne ƙashin bayan nagartacciyar dimokraɗiyya.
Wannan dimokraɗiyya ta na da kwarjini, nagarta da kuma armashi, domin ta bayar da dama duk wanda ya ke ganin an yi masa rashin adalci, zai iya matsawa gaba ya ɗaukaka ƙara, kotu ta karɓar masa haƙƙin sa.
“Saboda haka ina roƙon da wanda ya kai ƙara da wanda aka kai, su riƙa yin tawakkali su na karɓar hukuncin kotu da zuciya ɗaya. Domin ta haka ne za a gina ƙasaitacciyar Najeriya.”
Shugaba Buhari ya jinjina wa dukkan ‘yan takarar shugaban ƙasa a zaɓe, tare da cewa sun cancanci yabo ganin yadda su ka yi amanna da tsarin kotunan mu, har su ka garzaya kotu, bisa yaƙinin cewa za su yarda da sakamakon hukuncin da kotu za ta yanke.
“Ina taya aboki na na tsawon lokaci, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bisa samun nasarar da ya yi har ya cika burin sa rayuwa. Hakan kuwa ya tabbata ne saboda juriyar da ya daɗe ya na nunawa wajen gwagwagwar kishin Najeriya.”
Discussion about this post