Rundunar tsaro na Sibul Difens NSCDC dake jihar Kogi ta kama wani mahaifi mai shekaru 41 da ya rika lalata da ‘yar cikin sa a jihar Kogi.
Kwamandan hukumar Ahmed Gandi wanda ya sanar da haka yayin da yake gabatar da mutumin wa manema labarai a hedikwatar hukumar dake Lokoja ya ce rundunar ta kama mutumin ranar biyar ga Mayu bayan wata kungiya mai zaman kanta ta kawo kara a ofishinsu.
Gandi ya ce sakamakon binciken da suka gudanar ya nuna cewa mutumin ya fara yin lalata da ‘yarsa tun tana shekara 16 a 2020 zuwa 2023.
“Kanwar yarinyar ta bai wa yanta shawara su kashe kansu ko Kuma su kashe mahaifinsu domin raba kansu daga mahaifinsu.
Bayan haka yarinyar ta bayyana wa manema labarai cewa mahaifinta ya fara lalata tun bayan da mahaifiyarsa ta rabu da mahaifinsu.
“Mahaifina ya yi min ciki, da ya tabbata sai ya kaini wani asibiti aka cire ciki kuma ya ci gaba da yin lalata da ni.
“Kanwata ta bani shawaran na gudu amma ban iya guduwa saboda na san idan na gudu zai koma kan kanwata.
Ta ce da ta gaji shine ta Kai karar mahaifin nata kungiya mai zaman kansamai suna ‘Islamic Centre for Communication and Creative Thought (ItrippleCT)’.
Da ya shiga hannun jami’an tsaro mahaifin yarinyar ya tabbatar da aikata abin da ake tuhumar sa akai, amma ya roki sassauci cewa wai sheɗan ne ya ziga shi.