Gwamnan Zamfara mai barin gado, Bello Matawalle ya yi kira ga Hukumar EFCC ta binciki jami’an Fadar Shugaban Ƙasa da Ministocin Najeriya.
Jami’an Fadar Shugaban Ƙasa dai sun haɗa da Shugaban Ƙasa, Mataimakin Shugaban Ƙasa, sai ma’aikata da hadiman su.
Mambobin Majalisar Zartaswa da Matawalle ke so a bincika dai su ne Ministoci.
Matawalle ya bayyana haka a cikin wata sanarwa wadda ya ke magana kan binciken su gwamnoni masu barin gado da EFCC ke yi.
Ina roƙon EFCC kada binciken ta ya tsaya kan gwamnoni masu barin gado kaɗai. EFCC ta faɗaɗa binciken ta har kan manyan jami’an Fadar Shugaban Ƙasa da Ministoci na Majalisar Zartaswa.””
Matawalle zai sauka daga mulki ranar 29 Ga Mayu, bayan ya yi shekaru huɗu. Ya sake tsayawa takarar gwamna, amma Dauda Lawal na PDP ya raɗa shi da ƙasa.
Shi kan sa Matawalle ya na da matsala da EFCC, wadda a watannin baya ta ƙwace masa kantama kantaman kadarori masu tarin yawa na biliyoyin nairori.
Sai dai Babbar Kotun Tarayya ta ƙi yanke masa hukunci saboda ya na da rigar sulken kariyar da ya ke da ita, a matsayin sa na Gwamna.
Ana ganin Matawalle ne na farko-farkon waɗanda EFCC za su fara damƙewa bayan sun sauka a ƙarshen watan nan.
Farkon makon nan ne kuma Matawalle ya ce idan ka amince Emefiele ya tafi karatu waje, guduwa zai yi.
Gwamna mai barin gado na Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya roƙi Shugaba Muhammadu Buhari cewa kada ya rattaba hannun amincewa Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya tafi karatu ƙasar waje.
Cikin wata sanarwa da ya fitar ga PREMIUM TIMES, Matawalle ya ce Emefiele ya na neman samun damar arcewa ya bar ƙasar ce kafin ƙarshen mulkin Buhari, “domin ya kauce wa titsiyewar da za a yi masa” dangane da bayani dalla-dalla kan abin da ya faru a CBN a ƙarƙashin mulkin Emefiele ɗin.
Gwamnan CBN ne mai sa-ido kan harkokin kuɗaɗe. Shi ne algungumin da ya kitsa tsarin sauya launin kuɗi da ƙwace wa mutane kuɗaɗen hannun. Wannan lamari kuwa ya haddasa matsanancin ƙuncin rayuwa a cikin Najeriya baki ɗaya.
“Amma kuma wai yanzu wannan Emefiele ɗin ne ke neman amincewa ya tafi hutun zuwa Turai karatu, alhali ya na da saura watanni 10 kafin ya cika wa’adin sa.
“Ƙarya ya ke yi, ya ƙirƙiri shirin tafiya karatu waje ne don kada gwamnati mai hawa ta titsiye shi yin bayanin gidogar da ya yi a CBN.”
Har yanzu dai ba a ji daga bakin Emefiele ko CBN ba cewa Gwamnan zai fice idan Buhari ya ba shi dama ba.
Miliyoyin mutane a faɗin ƙasar nan sun ɗora wa Emefiele laifin wahala da ƙuncin da aka shiga a farkon shekarar nan, saboda sauya launin kuɗi.
Wata gagarimar matsala baya ga canji kuɗi da Emefiele ya haifar wa ƙasar nan, ita ce yadda ya bai wa Gwamnatin Buhari kuɗaɗen CBN bashi har na naira tiriliyan 23.7, ba tare da sanin Majalisar Dattawa da ta Tarayya ba
Hakan ya haifar da Gwamnatin Buhari za ta sauka ta bar bashin naira tiriliyan 23.7 da karɓa ba bisa ƙa’ida ba a CBN.
A farkon watan Janairu ne wannan jaridar ta buga bayanin cewa zaune ta tashi tsaye a Majalisar Dattawan Najeriya, yayin da su ka gano cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bai wa Gwamnatin Buhari ramcen tsabar kuɗi har naira tiriliyan 23.8 a cikin shekaru bakwai, ba bisa ƙa’ida ba.
Yadda Aka Bankaɗo Rufa-rufar:
A ranar Laraba ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ƙoƙarin neman amincewar Majalisar Dattawa ta sa hannu cewa ta amince CBN ta bayar da bashin, wanda an rigaya an karɓa, har an dagargaje kuɗaɗen. Shi ne maimakon gwamnatin Buhari ta nemi amincewar Majalisar Dattawa, sai yanzu ta nema a makare, bayan an karɓa, an kashe tuni.
Na farko dai gwamnatin Buhari ki kuma a ce Shugaba Buhari ya karya doka, saboda ya yi ta karɓar kuɗaɗen daga CBN ba tare da neman amincewar Majalisar Dattawa ba.
Na biyu, CBN da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele sun karya doka, domin sun bai wa Gwamantin Buahri bashin da ya wuce ƙa’idar da ya kamata a bayar har sau 2900%.
Adadin Nawa Dokar Najeriya Ta Ce CBN Ya Ramta Wa Gwamnatin Tarayya?:
Dokar CBN ta cikin Kundin Dokokin Najeriya ta ce, “idan gwamnatin tarayya na fama da giɓin kasafin kuɗaɗe, za ta iya ramcen kuɗi daga CBN. Amma adadin da CBN zai bayar kada ya wuce kashi 5% kacal na jimlar kuɗaɗen shigar da gwamnatin tarayya ta samu a shekarar da ta gabata.”
Illar Wannan Bashin Rufa-rufa:
Wannan bashi a gwamnatin Buhari ta ci daga CBN ba bisa ƙa’ida ba, ya karya doka, ya haifar da tsadar rayuwa, ƙuncin rayuwa, hauhawar farashi, gurguncewar tattalin arziki da kuma jibga ɗimbin bashi a wuyan kowane ɗan Najeriya, har waɗanda za a haifa nan da shekaru masu zuwa.
Bashin Nawa Buhari Ya Gada Daga CBN:
Lokacin da Buhari ya hau mulki a Mayu, 2015, ya taras da bashin naira biliyan 789.7 da gwamnatin baya ta ciwo daga CBN.
Amma tsakanin Janairu zuwa Oktoba 2022, kaɗai a wannan shekarar, Gwamnatin Buhari ta ciwo bashin naira tiriliyan 5.6 daga CBN.
Tsakanin 2012 zuwa Mayu, 2015 kafin hawan Buhari, CBN na bin gwamnatin tarayya bashi na naira biliyan 654.9 kacal.
Ƙa’idar Karɓar Bashin CBN:
Dokar Najeriya cewa ta yi, “Gwamnatin Tarayya ta riƙa gaggauta biyan bashin da ta karɓa kafin ƙarshen shekarar
da ta karɓi bashin. Ko kuma kafin sake karɓar wani sabon bashin.”
Sai dai kuma duk Gwamnan CBN Godwin Emefiele da Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Ahmed sun sa ƙafa sun take wannan doka.
A Ƙa’ida, Bashin Naira Biliyan 219 Ya Kamata CBN Ya Ba Gwamantin Buhari A 2022, Ba Naira Tiriliyan 5 Ba:
Saboda naira biliyan 219 su ne kashi 5% na adadin kuɗaɗen shigar da gwamnatin tarayya ta samu a shekarar 2021.
Yadda Gwamnatin Buhari Ta Riƙa Karɓar Bashin CBN:
CIkin 2017 har bashin da CBN ke bi ya kai naira tiriliyan 3.3.
Zuwa Disamba 2018 kuma bashin ya kai Naira tiriliyan 5.4, zuwa Disamba 2019 kuwa ya kai naira tiriliyan 8.7.
Zuwa Disamba 2020 bashin ya cilla sama har zuwa
naira tiriliyan 13.1. Zuwa Disamba 2021 ya kai Naira tiriliyan 17.4.
Yanzu kuwa zuwa Disamba 2022, bashin ya kai naira tiriliyan 23.8, kuma ko sisi gwamnati ba ta taɓa ko fara biya ba.
Bashin Da Ko Gwamnatin Jikokin Mu Ba Za Su Iya Biya Ba:
Cikin watan Oktoba 2022 ne Gwamnatin Tarayya ta rattaba cewa sai nan da shekaru 40 za a kammala biyan bashin, a kan kuɗin ruwa na kashi 9%. Kenan babu ruwan gwamnatin Buhari ya jeƙala-jeƙalar biyan bashin.
Tuni dai Majalisar Dattawa ta ce a binciki ayyukan da aka ce an yi da kuɗin.
A gefe ɗaya kuwa masu sharhi na cewa hatta sabbin kuɗaɗen da CBN ya buga, duk wata rufa-rufa ce kawai.
Jefa Tattalin Arziki Cikin Tarangahuma:
Yadda Majalisa Ta Amince A Shafe Shekaru 40 Ana Biyan Bashin Naira Tiriliyan Da Gwamnatin Buhari Ta Karɓa A CBN:
Majalisar Tarayya ta amince kada a biya bashin Naira tiriliyan 23.7 da Buhari ya karɓa a CBN, sai nan da shekaru 40.
Majalisar Wakilai ta Ƙasa ta amince da buƙatar da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar mata a cikin 2022, cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta kammala biyan bashin naira tiriliyan 22.7 da ya ciwo a Babban Bankin Najeriya ba, sai nan da shekaru 40.
Wannan amincewa ta zo ne daidai lokacin da ɗimbin bashi ta ko’ina ya yi wa gwamnatin tarayya katutu.
A cikin makon nan ne kuma Gwamna Obaseki na Jihar Edo ya bayyana cewa daga watan Yuni gwamnatocin Tarayya da na jihohi ba za su iya biyan albashi ba, sai fa idan an cire tallafin fetur. Cire tallafin fetur kuwa zai iya sa a riƙa sayen kowace lita ɗaya wajen Naira 500 ko sama da haka.
Awannan makon kuma Majalisa ta amince a jinkirta kammala biyan bashin naira tiriliyan 22.7 da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta karɓa a CBN zuwa nan da shekaru 40 masu zuwa.
A ranar Alhamis ce su ka amince da wannan tsarin, bayan yin nazarin rahoton da Kwamitin Majalisa kan Harkokin Kuɗaɗe, Banki, Tallafi, Basussuka da Ramce su ya gabatar.
Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya, Idris Wase ya amince da shawarwarin da kwamitin ya gabatar, kuma ya rattaba masu hannu.
Buhari dai zai sauka a ranar 29 Ga Mayu, ya nemi a maida biyan bashin na Naira tiriliyan 22.7 zuwa nan da shekaru 40.
A cikin Nuwamba 2022 ɗin ne kuma Buhari ya nemi amincewa ya ciwo bashin Naira tiriliyan 1, domin amfani da su a ƙarin kasafin Naira biliyan 819.5 na 2022. Shi wannan bashin tun a cikin watan Disamba su ka amince a karɓo shi.
‘Yan Najeriya da dama sun ce bashin Naira tiriliyan 22.7 da Buhari ya karɓa a CBN ba ya cikin doka. Kuma sun yi mamakin yadda aka nemi bashin, kuma aka bayar ba tare da tuntuɓar Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya ba.
Idan za a tuna, a farkon watan Fabrairu, Atiku ya ce Buhari ne sanadin ɗora Najeriya a koma bayan lalatattun ƙasashe.
Ɗan takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin PDP, Atiku Abubakar ya ce laifin Buhari ne da ƙasar nan ta tsinci kan ta a jerin ƙasashen da ke fama da gigitaccen tattalin arzikin ƙasa.
Atiku ya ce idan ya zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023, zai hanzarta wajen ceto tattalin arzikin Najeriya daga cikin kwatamin da Buhari ya jefa shi.
Atiku ya yi wannan bayani ne cikin wata sanarwa bayan da aka fitar da alƙaluman ɗimbin bashi da koma bayan hada-hadar bunƙasa tattalin arziki, wanda Najeriya ta tsinci kan ta a ciki.
Cikin makon jiya ne wata ƙungiya mai ƙididdigar ɗora ƙasashe bisa mizanin awon koma bayan tattalin arzikin ƙasa ya ce Najeriya ta samu gagarumin koma baya ta fuskar matsalar kuɗaɗe da ɗimbin basussuka.
Mizanin awon ya nuna Najeriya za ta ci gaba da fuskantar wannan mawuyacin hali, a matsayin ta babba a tattalin arzikin ƙasashen Afrika.
Zazzafa Daga Atiku Zuwa Ga Buhari: Mugun zarin ka na rashin ƙyamar ciwo bashi ko a ina ne ya sa ka kasa rage giɓin kasafin kuɗi a duk shekara. Sai ka ɓuge wajen ɗibga babban kuskuren rika ciwo bashin Bankin CBN. To yanzu ga shi nan ka kai ƙasar ka baro.”
“Saboda haka ni idan aka ba ni damar saisaita tattalin arzikin Najeriya. Ida da idanu garau, ba makahon da ko ɗan jagora ba shi da shi ba ne. Zan yi ƙoƙarin tabbatar da dawo da tattalin arzikin Najeriya ciki hayyacin sa.” Inji Atiku.