Gwamnatin Jihar Katsina ta yi wa fitaccen mawaƙi Dauda Kahutu da aka fi sani Rarara tallafin Naira miliyan 50, shi kuma abokin sa Baban Chinedu naira miliyan 30.
Su biyun dai duk ‘yan asalin Jihar Katsina ne, da ke harkokin waƙoƙi da alaƙar ‘yan fim a Kano.
An ba su kuɗaɗen domin biyan su asarar da su ka ɗibga biyo bayan harin banka wuta da hasalallun matasa su ka kai wa kadarorin su a Kano, bayan bayyana nasarar da ɗan takarar gwamna na NNPP, Abba Yusuf, da aka fi sani da Gida-gida ya yi a Kano.
Baban Chinedu da Rarara dai duk mawaƙan APC ne, kuma mabiya ɗariƙar siyasar Gandujiyya.
Mafusata sun banka wa gida da ofishin Rarara wuta, kuma aka riƙa jidar dukiya ana tserewa da ita.
An kai wa Rarara hari ne sanadiyyar wata waƙa da ya saki wajen ƙarfe biyu na dare, mai ɗauke da baitocin da ke nuna cewa Nasir Gawuna ɗan takarar APC ya lashe zaɓen Kano.
Rarara ya saki waƙar a daidai lokacin da an kammala ƙidayar dukkan ƙananan hukumomi, sakamakon zaɓe kaɗai ya rage a bayyana, kuma Abba na NNPP ya yi wa Gawuna ratar ƙuri’u sama da 120,000.
Bayan bayyana sakamakon zaɓen ne da safe mafusata su ka tunzura su ka riƙa ragargazar gida da ofishin Rarara, lamarin da ya haifar masa mummunar asara, shi da Baban Chinedu.
Wata wasiƙar da ke yawo a soshiyal midiya na ɗauke da bayanin kyautar Naira miliyan 80 da Gwamnatin Jihar Katsina ta bai wa Rarara da Baban Chinedu.
“Ina mai umartar ka cewa ka fitar da kuɗi naira miliyan 80, ka bai wa Sakataren Gwamnatin Katsina, a matsayin tallafi ga Abdullahi Adamu Rarara da Baban Chinedu, domin su samar wa kan su muhallin zama, bayan ƙona masu gida da kadarori da aka yi a hargitsin siyasa, a Kano, ranar 20 Ga Maris, 2023.
“Za a bai wa Rarara miliyan 50, shi kuma Baban Chinedu miliyan 30.”
Wakilin mu ya nemi jin ta bakin Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan Katsina, Al’amin Isa, wanda ya ce a ba shi lokaci ya tabbatar da sahihancin wasiƙar tukunna.
Discussion about this post