Gwamnatin Tarayya ta rattaba hannun amincewa da fara sabbin tsare-tsaren 2023, wanda a ƙarƙashin su ne aka ƙara kuɗin haraji kan nau’in ruwan kwalba masu bugarwa da su ka haɗa da barasa, giya da ‘wine’.
Haka kuma an ƙara haraji kan kowane karan taba sigari na kowace irin tabar da ake sha hayaƙi na tashi.
Haka kuma gwamnati ta ƙara haraji kan kayayyakin da su ka danganci nau’in robobi.
Sanarwar da ta fito mai lamba HMFBNP/MDAs/2023 FP004, ta ranar 20 Ga Afrilu, 2023, wadda Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed ta sa wa hannu, an ƙara Naira 75 kan kowace lita ɗaya ta giya da sauran nau’in barasar ‘beer’, ‘stout’ da ‘wine’.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya amince da yin wannan ƙarin.
In dai wani nau’in ruwan kiri ko wanda ake tsimawa ne ko wanda ba a taimawa, to ƙarin ya shafe shi. Sai fa wanda ake sarrafawa a ‘Malt’ kaɗai.
“Daga ranar 1 Ga Yuni kuma an ƙara haraji kan motocin da ake shigowa da su. Akwai waɗanda aka ƙara wa kashi 2 bisa 100, wasu kuma 4 bisa 100.
Discussion about this post