Zazzafan rikici ya ɓarke tsakanin Gwamnatin Tarayya da Gwamna Nasiru El-Rufai, sakamakon zargin da tarayya ta yi cewa gwamnatin Kaduna ta yi cin-iyaka, ta shiga cikin filin Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Malali, a Kaduna.
Duk da cewa saura kwanaki 19 El-Rufai ya sauka daga mulkin jihar Kaduna, Ma’aikatar Ilmi ta Tarayya ta garzaya kotu, inda ta samo sammacin umarnin hanawa ko dakatar da gwamnatin jihar Kaduna da ci gaba da gine-gine a cikin filin kwalejin tarayya ta Malali.
Mai Shari’a B.F Zubairu na Babbar Kotun Kaduna ne dai tun a ranar 2 Ga Mayu, ya amshi roƙon Ma’aikatar Ilmi ta Tarayya, inda ya umarci Gwamnatin Jihar Kaduna cewa, “ta daina shiga, ta daina gine-gine ko gilmawa ta cikin fili mallakar Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Malali.”
Bayan Ma’aikatar Ilmi ta samu wannan umarnin da ta ke nema a kotu, sai ta garzaya ta rubuta wasiƙa ga Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Alƙali Usman.
Takardar mai lambar kwafe: FME/LU/HQ/S/434/23/1/53, wadda aka rubuta a ranar 5 Ga Mayu, ta nemi ya tura zaratan ‘yan sanda don su hana gwamnatin Kaduna ci gaba da gine-gine a cikin filin kwalejin.
Babban Sakataren Ma’aikatar Ilmi, Andrew Adejo ne ya rubuta wasiƙar mai ɗauke da roƙon “a tura ‘yan sanda a wurin da gwamnatin Kaduna ke aikace-aikace a cikin filin Kwalejin Tarayya ta Malali, domin a kare ƙananan yara da dukiya da kadarorin kwalejin.”
Tun da farko dai Ƙungiyar Tsoffin Ɗalibai na Kwalejin Tarayya ta Malali ne su ka zargi gwamnatin jihar Kaduna da shiga cikin filin Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Malali, kuma ta yi kira ga hukuma ta shiga lamarin.
Kungiyar ta ce tun cikin 2015 gwamnatin Kaduna ta nemi Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ɗan kamfatar mata wani wuri daga cikin filin Kwalejin domin ta yi wani gini a ciki. Amma ma’aikatar ilmi ba ta amince ba.
Gwamnatin Tarayya kuma ta zargi gwamnatin El-Rufai da rushe wani sashe na bangon kwalejin, lamarin da tarayya ta ce tamkar yaran na cikin barazanar yiwuwar kai masu harin ta’addanci.
Sai dai kuma duk da umarnin da kotu ta bayar, Gwamantin Kaduna ba ta tsaida gine-ginen da ta fara a cikin kwalejin ba.” Haka dai Shugaban Ƙungiyar Tsoffin Ɗalibai ɗin, Seyi Gambo ya shaida wa PREMIUM TIMES.
Gambo ya ce har cikin makon jiya gwamnatin El-Rufai ta ci gaba da gini a cikin kwalejin.
Gambo ya zargi ‘yan sanda da ɗaure wa gwamnatin El-Rufai gindi. Domin cewa su ke yi wai su na binciken lamarin, alhali kuma ga shi a gaban su ake ci gaba da gine-gine.
Sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan Kaduna’ ya ce bai daɗe da komawa aiki zuwa Jihar Kaduna ba. Amma dai ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa a za bincika, kuma za a yi adalci wajen bin umarnin kotu.
Sakataren Yaɗa Labaran Gwamna El-Rufai, Ibrahim Musa, ya ƙi cewa komai.
Discussion about this post