Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya, Idris Wase, ya fito ƙiri-ƙiri ya yi fatali da matsayar da APC da Tinubu su ka ɗauka, inda su ka bada shugabancin Kakakin Majalisar Tarayya ga Tajuddeen Abbas na Jihar Kaduna.
Wase, wanda a yanzu shi ne Mataimakin Femi Gbajabiamila tsawon shekaru huɗu, ya bayyana cewa shi ma yanzu lokacin da ne da zai zama Kakakin Majalisar Tarayya.
Ya bayyana haka ranar Juma’a, a otal ɗin Transcorp Hilton, Abuja, inda a jawabin sa, ya ce shi ma ya ari salon da Bola Tinubu ya yi, na ‘Emi lokon’, ya ce “Ni ma yanzu ne lokaci na.”
“A wannan lokacin, zan ari salon karin maganar da oga na Bola Tinubu ya yi amfani da ita, ’emi lokan, emi lokan, emi lokan,” ya maimaita sau uku, watau “yanzu lokaci ɗaya ne.”
Wase wanda ya fito daga jihar Filato, ya ce tilas jam’iyya mai mulki ta bi tsarin da dokokin tsarin mulkin Najeriya ya shimfiɗa, ta yadda za su tabbatar da cewa ba a maida yankin su na Arewa ta Tsakiya saniyar-ware ba.
“Ya kamata a lura da cewa yankin Arewa ta Tsakiya ne kaɗai bai taɓa samar da Kakakin Majalisar Tarayya a Najeriya ba, tun daga komawar dimokraɗiyya cikin 1999 har zuwa 2023.
‘Za Mu Fito Da Wanda Zai Zama Kakakin Majalisar Tarayya’ – Betara:
Ɗaya daga cikin masu neman kujerar shugabancin majalisar tarayya, Betara, ya ce su ne za su zaɓi wanda zai zama Kakakin Majalisar Tarayya.
Ya bayyana haka a wurin ƙaddamar da takarar Idris Wase.
Ya ce babu yadda za a yi a cewa wai APC ce da wasu gungun mutane za su zaɓi wanda zai zama Kakakin Majalisar Tarayya, ba tare da tuntuɓar ‘yan majalisa ba.
Discussion about this post