Gogarman ƴan bindiga Dogo Giɗe ya ƙara sakin ɗaliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Yauri uku daga cikin sauran 11 da su ka rage a hannun sa tsawon shekaru biyu bayan garkuwa da su.
An yi garkuwa da ɗimbin ɗaliban kwalejin ne tun a cikin watan Yuni na 2021.
Jiya Litinin ce aka sako uku ɗin, bayan an saki wasu huɗu makonni uku da su ka gabata.
An saki huɗu na kwanakin baya, bayan an biya kuɗin fansa naira miliyan 80.
Shugaban Ƙungiyar iyayen da aka yi garkuwa da ‘ya’yan sa, Salim Kaoje, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES sakin ɗaliban mata su uku a ranar Litinin.
Waɗanda aka saki ɗin haɗa da Aliya Abubakar, Esther Sunday da kuma Elizabeth Nwafor.
Kaoje wanda har yanzu ƙanuwar su na can riƙe a hannun ‘yan bindiga, ya ce Giɗe ya ƙara sakin matan uku ne ba tare da nemi a ƙara biyan sa ko sisi ba.
Tun da farko dai sama da ɗalibai 100 aka yi garkuwa da su, tare da wasu malaman kwalejin.
Yayin da wasu su ka kuɓuta, an saki wasu da dama bayan an biya kuɗin fansa. Wasu kuma an sake su ne bayan gwamnati ta saki wasu mayaƙan Dogo Giɗe da aka tsare.
Sauran mata 11 su ka rage a hannun su. Yanzu sun ƙara sakin uku, saura takwas kenan.
Tuni dai aka garzaya da matan Gidan Gwamnatin Jihar Kebbi, a Birnin Kebbi.
Discussion about this post