Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdulahi Ganduje, ya bayyana cewa a tsawon shekaru takwas na mulkin sa, Jihar Kano ta karɓi Naira tiriliyan 1.2.
Ya ce baya ga wannan kuma, zai tafi ya bar bashin Naira biliyan 241.
Ganduje ya bayyana haka ta bakin Sakataren Gwamnatin Kano, wanda ya wakilce shi wurin miƙa mulki, ranar Lahadi, a gidan Gwamnatin Kano.
Sai dai kuma sabon Gwamna Abba Kabir-Yusuf, ya nuna rashin jin daɗin yadda Ganduje ya ƙi halartar miƙa mulkin, kamar yadda aka saba a al’adance.
Dangane da bashin da zai gada daga hannun Ganduje kuwa, ya yi gwamnatin sa za ta yi nazarin basussukan, tare da bin-diddigin yadda aka ciwo su, sannan daga baya ta bayyana matsayin ta a kan basussukan.
Ganduje da mataimakin sa dai ba su tsaya Kano ba, sun je Abuja ne wurin rantsar da Tinubu.
Sai dai kuma wakilin mu ya hangi jami’an tsaro sun hana shi shiga ɓangaren wasu manyan baƙi a dandalin rantsuwar.
An hange shi a wurin taron shi da matar sa, Gwaggo, sun yi tsuru-tsuru a cikin taro.
Discussion about this post