Kotun dake sauraren kararrakin cin zarafin mata da yara kanana dake Ikeja jihar Legas ta yanke wa Sunday George mai shekara 26 hukuncin daurin rai da rai bayan an kama shi da laifin yi wa ‘yar makwabcin sa mai shekara 12 fyade.
Alkalin kotun Abiola Soladoye ya ce ya yanke wannan hukunci ne bayan fannin da ta shigar da kara ta tabbatar wa kotun cewa George ya aikata laifin da ake zargin sa akai.
“Yarinyar ta bayyana cewa George makwabcin su ne kuma ya fara yin lalata ta ita a dakin sa tare da ja mata kunnen kada ta fadi wa kowa.
“George ya ci gaba da danne wannan yarinya a cikin dakinsa idan ta shigo kallon talabijin.
“Mahaifin yarinyar da yarinyar suka kai kara ofishin ‘yan sandan sannan kotun ta samu tabbacin abin da George ya aikata daga hujjojin da rundunar ‘yan sandan ta gabatar.
“Kotu ta fahimci cewa George makaryaci, malalacin mutum ne da ya shahara wajen yi wa yara kanana fyade.
Soladoye ya yi kira ga gwamnati da ta ci gaba da yin kira ga iyaye kan samin mahimmancin maida hankali da kula da ‘ya’yan su domin guje wa afkawa matsaloli irin haka.