A ranar Lahadi ne jama’a suka afka cikin ruɗani da fargaba a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja bayan da wani jirgin saman Max Air ya yi saukar gaggawa a filin.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na rana. kuma ba a samu asarar rai ba, kamar yadda PREMIUM TIMES ta jiyo.
Wasu majiyoyi a filin jirgin da suka nemi a sakaya sunayensu saboda ba su da izinin yin magana a kan lamarin sun ce lamarin ya hana zirga-zirgar jiragen sama da dama da ke sauka a filin.
Bayan haka wasu fasinjoji dun shaida cewa an samu jinkiri wajen tashin jirgin su da zai sauka a Abuja saboda hatsarin da aka yi.
Amma kuma mahukunta sun shaida cewa ba a samu ko da mutum ɗaya da ya samu do da kurzina bane a yayin wannan hatsari. Duka fasinjoji sun sauka lafiya
Mahukunta sun ce tayouyin jirgin ne suka fashe a lokacin da yake kokarin sauka a filin Abuja. Amma kuma cikin gaggawa Injiniyoyi suka dira wa lamarin har aka samu shawo kansa cikin sauki.
Jirgin saman ya taso me daga Yola zuwa Abuja.
Discussion about this post