Shugaban rukunin jami’o’in Maryam Abacha da ke Nijar da Najeriya, Farfesa Adamu Gwarzo ya kai ziyarar taya murna ga zaɓaɓɓen gwamnan Zamfara, Dauda Lawal a cikin makon jiya.
A lokacin ziyarar Farfesa Gwarzo ya mika gaisuwar sa da taya shi murna sannan kuma ya yi wa zaɓabben gwamnan fatan alkhairi da yi masa adduar Allah ya bashi nasara a tsawon mulkin sa.
” Jama’a sun zaɓe ka, fatan mu shine Allah ya baka ikon cika alkawuran da ka dauka duka, Allah ya yi maka jagora domin a sanin da kai, kai gogan aiki ne mai taimako da tausayin talaka.” In ji Gwarzo.
A jawabin sa, Lawal ya yi alkawarin tabbatar da ingantaccen mulki a jihar, da kuma kawo karshen matsalolin da jihar Zamfara ke fama dashi.
Idan ba manta ba Dauda Lawal na jam’iyyar PDP ya lashe zaben gwamnan jihar Zamfara a zaɓen watan Maris.
Wannan nasara da ya samu yayi matuƙar baiwa mutane da dama mamakin gaske ganin irin kurin da gwamna mai ci Bello Matawalle ya rika yi kafin zaɓen.
Farfesa Gwarzo wanda fitacce ne musamman wajen bunkasa fannin ilimi a yankin Arewa, Najeriya da Afrika baki daya.
Gudunmawar da ya baiwa fannin ilimi a kasar nan da nahiyar Afrika ba shi misaltuwa. Baya ga jami’o’i wanda shi da kansa ya gina su, ya na tallafa wa har da jami’o’in gwamnatin tarayya da na jihohi harda ma masu zaman kansu domin a samu wanzuwar ilimi a ko’ina.
Baya ga tallafi da yake baiwa yayan musammam talakawa ya na a ko ina shirye yake domin bada kowani irin gudunmawa ake bukata domin ci gaban al’umma da wanzuwar Ilimi.
Discussion about this post