Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta umarci gwamnati mai barin gado ta Shugaba Muhammadu Buhari ta yi bayanin yadda ta yi da dala miliyan 460, waɗanda aka karɓo bashi daga Chana domin ta kafa kyamarar CCTV mai tantance mugu a cikin nagari a Abuja, aikin da aka ce ba a yi ba, kuma ba a san yadda aka yi da kuɗin ba.
Haka kuma kotun ta umarci Gwamnatin Buhari ta gaggauta shiga shafukan jaridu ta bayyana adadin yawan kuɗin da aka maida a matsayin biyan bashin, idan har an biya ko an fara biyan.
Kuma an nemi Gwamantin Buhari ta bayyana sunayen kamfanonin da aka ba kwangilar, da sunayen ‘yan kwangilar da kuma iyar inda aikin ya tsaya.
Mai Shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da wannan umarnin a ranar Litinin, 15 ga Mayu, a matsayin hukuncin da ya yanke na wata ƙarar da aka shigar ta haƙƙin neman bayani daga gwamnati, wanda ‘yan Najeriya ke da ‘yancin su nemi ta yi masu.
Ƙungiyar Rashin Hana Rashawa ta SERAP ce ta shigar da Gwamnatin Buhari ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara, Abuja.
SERAP ɗin ce kuma ta aiko wa PREMIUM TIMES kwafen hukincin wanda kotun ta yanke.
Yadda Aka Ciwo Bashin, Kuma Aka Ƙi Yin Aikin:
Gwamnatin Buhari ta ciwo bashin dala miliyan 460 daga Chana cikin 2010, a lokacin tsohon Ministan Harkokin Kuɗaɗe na lokacin, Olusegun Aganga.
Shi ne ma ya ja zugar tawagar da su ka je takanas har Chana, ya sa hannu kan bashin, a birnin Beijing.
Za a yi aikin ne daga dala miliyan 600 ɗin da aka ramta daga Chana ɗin.
Rahoto ya ce ramcen da aka yi na kuɗaɗen, za a riƙa biyan kuɗin ruwa har tsawon shekara 10, kuma sai an yi shekara 10 da karɓar lamunin sannan za a fara biyan lamunin.
Yayin da aikin liƙa CCTV ɗin Abuja ya shiririce, a gefe ɗaya kuma matsalar tsaro ta ƙasa sukurkucewa a babban birnin a Najeriya.
Amma duk da haka, Najeriya ta ci gaba da biyan kuɗin lamunin yayin da gwamnatin Buhari wadda ta gaji bashin, ta ƙi yi wa ‘yan Najeriya bayanin yadda aka yi da zunzurutun kuɗin.
“Bashin dai kam mu na ci gaba da biya, amma fa batun an yi aikin ko ba a yi wa, sai dai mu tambayi Hukumar FCT Abuja ta yi bayanin inda aka tsaya. Saboda Ni dai ban san komai a kai ba.” Inji Zainab Ahmed, Ministar Harkokin Kuɗaɗe.
Haka Zainab ta bayyana lokacin da take amsa tambayoyi a gaban Kwamitin Majalisar Tarayya na Ayyukan Tsaro, a cikin Oktoba, 2019.
Ganin cewa Minsita Zainab ta kasa bayar da amsa tun a cikin 2019, sannan kuma akwai zargin ciwo wani bashi na Naira biliyan 1.5 wanda aka gina Hedikwatar CCB, sai SERAP ta nemi Minista Zainab ta yi bayanin yadda aka yi da kuɗaɗen.
Ganin cewa Zainab ta ƙi bai wa SERAP bayani, sai ƙungiyar ta maka gwamnati ƙara, a cikin 2029, a ƙara mai lamba ABJ/CS/1447/2017, ta na neman kotu ta tilasta wa gwamnatin Buhari ko Minista Zainab su bayyana mata yadda aka yi da kuɗaɗen.
A kotu dai Minista Zainab ta ce ba ta samu wasiƙar da SERAP ta ce ta aika mata ba, shi ya sa ba ta yi wa ƙungiyar bayani ba, tun a 2019 ɗin.
SERAP ta gabatar wa kotu hujjar cewa Zainab ta karɓi wasiƙar, wadda ta aika mata ta UPS.
Mai Shari’a ya umarci Gwamnatin Buhari ta hannun Ministar Harkokin Kuɗaɗe ta bayar da bayanin komai dalla-dalla.
Discussion about this post