Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan a ranar Asabar ya bayyana cewa tabbas zai amince da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a Kasar ranar Lahadi, kuma zai sauka daga mulki idan ma ya sha kaye, yana mai karyata fargaba da rade-radin da ake yi wai ba zai mika mulki ba idan ya fadi zabe.
Da yake amsa tambayar ko wai ba zai mika mulki ba idan ya sha kayi a zaben Erdoğan ya ce ” Wannan tambaya a ganina wauta ce, ko kuma in ce ba shi da amfani yin sa domin ta hanyar dimokradiyya muka dare kujerar mulki a Turkiya, Me zai hana idan mutane turkiyya suka canja shawara yanzu ba su zabe mu ba, zan yi kamar yadda dimokradiyya ta gindaya. Babu wani abinda zai yi da ya wuce hak.
Erdoğan ya ce da shi da magoya bayan sa a shirye suke su bi abinda mutane suka zaba. Daga nan sai ya yi kira ga ‘yan adawa da su saka mutane su kula musu da akwatunan zabe maimakon babatu da suke ta yi da zarge-zarge.
” Kira na ga ‘yan adawa shine su saka mutane a duk inda ake zabe domin su kula musu da yadda ake kada kuri’a. Domin ba za mu yarda a kawo mana jagwalgwalo a zaben mu ba. Abinda mutane suka zaba shi za a ba su.