Hukumar EFCC ta tsare tsohon Ministan Harkokin Makamashi da Lantarki, Sale Mamman.
EFCC na zargin Mamman da karkatar da naira biliyan 22.
Wata majiyar da ba ta so PREMIUM TIMES ta ambaci sunan ta, ta bayyana cewa an tsare Mamman a ranar Laraba bayan ya kai kan sa Hedikwatar EFCC, bisa amsa gayyatar da aka yi masa.
Mamman ya zama Ministan Lantarki daga Agusta 2019 zuwa Satumba, 2021.
Sai dai kuma ba zato ba tsammani Shugaba Muhammadu Buhari ya cire shi.
Majiya ta shaida wa wannan jarida cewa Mamman ya haɗa baki da wasu manyan jami’an Ma’aikatar Lantarki su ka karkatar da naira biliyan 22, sannan su ka yi watandar ta a tsakanin su.
Majiyar ta ce sun haɗa baki sun kacaccala naira biliyan 22 a tsakanin su, kuɗaɗen aikin tashar wutar lantarki ta Zungeru.
Majiya ta ƙara da cewa bincike ya gano Mamman ya sayi maka-makan kadarori a cikin Najeriya da ƙasashen waje.
Sannan kuma an an fara kwato maƙudan kuɗaɗe na Naira da daloli.”
Discussion about this post