Tsohuwar Ministar Harkokin Fetur a zamanin mulkin Goodluck Jonathan, Diezani Alison-Madueke, ta maka Ministan Harkokin Shari’a, kuma Antoni Janar na Tarayya da kuma Hukumar EFCC kotu.
Ta shigar da su ƙara ne saboda wasu bayanai da Antoni Janar ya wallafa, inda ta ce a cikin bayanan an kira ta da suna ɓarauniyar da ta sace maƙudan kuɗaɗen gwamnati.
Diezani ta na nan Antoni Janar da EFCC su biya ta diyyar Naira biliyan 100, saboda an ɓata mata suna, cin mutuncin ta da zubar mata da ƙima a Najeriya da duniya baki ɗaya.
Ta ce sun yi mata sharri da ɓata mata suna cewa ita mai cin rashawa ce kuma wadda ta shahara wajen kwasar maƙudan kuɗaɗen gwamnati.
An shigar da ƙarar a Babbar Kotun Abuja a ranar 26 Ga Mayu, inda aka ƙalubalanci rahoton kwafen littafin da aka buga tun a 2016.
Ta shigar da ƙarar kwanaki uku saura cikar wa’adin Gwamnatin Shugaba Muhammadu, Buhari, gwamnatin da ta bijiro da binciken Diezani, tare da zargin ta sace maƙudan biliyoyin kuɗaɗe.
Diezani mai shekaru 62, ta gudu zuwa Birtaniya tun cikin 2015. Ta shigar da wannan ƙara a baya-bayan nan, ta hannun lauyan ta, Mike Ozekhome.
Ta na neman kotu ta ayyana cewa wasu zarge-zargen kiran ta ɓarauniya da aka buga a jaridu, shafin intanet na EFCC tsakanin 2016 zuwa 2022, cewa ƙarya da ƙage ne ake mata.
Baya ga neman diyyar naira biliyan 100 da ta ke yi, Diezani ta roƙi kotu ta tilasta wa EFCC da Ministan Shari’a su janye kiran ta ɓarauniya da su ka yi a jaridu. Kuma su ba ta haƙurin ɓata mata su na da su ka yi.
Ta nemi su buga sanarwar ba ta haƙuri da neman afuwa a jaridun THISDAY, The Punch da kuma The Sun cikin kwanaki bakwai daga ranar da kotu ta yanke hukuncin ba su umarnin yin haka ɗin.
Tun farkon hawan Buhari ne aka fara binciken Diezani, aka bada sammacin kamo ta duk inda ta ke. Amma dai shekaru takwas kenan abin ya gagara.
EFCC ta zargi gwamnatin Ingila da kare Diezani da hana maido ta Najeriya ta fuskanci hukunci.
Diezani ta ƙaryata zargin ta “an gano dala miliyan 72.8 da ta ɓoye a Fidelity Bank’.
An gano kuɗaɗen a ranar 16 Ga Disamba, 2021.
Kuma ta musanta cewa ta saci Naira biliyan 47.2, dala miliyan 487.5.
Kuma ta ce ƙarya ake yi mata, ba ta saci wata dala biliyan 2.5 da wasu naira bilyan 47.2.
Ba Gudu Na Yi Ba, Na Garzaya Ne Ganin Likita Ingila – Diezani:
Tsohuwar ministar dai ta ce ba gudu ta yi daga Najeriya ana saura mako ɗaya kafin saukar Goodluck Jonathan daga mulki.
Ta ce ta garzaya asibiti ne domin likitan ta ya duba lafiyar ta.
Discussion about this post