Kotun Ingila ta yanke wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ike Ekweremadu ɗaurin shekaru 9 da watanni 8 a kurkuku.
Haka kuma kotun ta ɗaure matar sa Beatrice ɗaurin shekaru 4 da wata 6, sai likitan sa likitan sa ɗaurin shekara 10.
An same su da laifin safarar wani matashin yaro daga Legas zuwa Landan, domin a cire ƙodar sa ɗaya a dasa wa Sonia, ‘yar Ekweremadu.
Mai Shari’a ya sallami Sonia, ya ce ba ta aikata laifin komai ba.
Sauran ukun kuma an same su da laifin yunƙurin yin dashen ƙoda ba bisa ƙa’ida ba.
A kotun dai an ga ‘yar Ekweremadu wato Sonia wadda ke fama da matsanancin ciwon ƙoda ta na ta darza kuka, bayan kotu ta sallame ta.
Mai Shari’a Johnson ya shaida wa masu laifin cewa: “Ku duka ukun laifukan ku sun yi tsananin da sun wuce a ci ku tara ko a litasta ku sharar titi kaɗai.”
An same su da laifin ɗauko yaro mai shekaru 21 daga Najeriya ba bisa ƙa’ida ba, su ka tafi da shi Landan, domin a cire ƙodar sa, a dasa wa Sonia, ‘yar Ekweremadu.
An shirya dai za a yi dashen ƙoda ɗin a wani asibiti mai zaman kan sa, kan fam 80,000 a Landan, mai suna Royal Free Hospital.
Su Ekweremadu ne farkon waɗanda aka taɓa ɗaurewa kan irin wannan laifi na safarar sassan jikin mutum a yi dashe a jikin wani mutum.
Yayin da doka ta amince wani ya taimaka wa wani da ƙodar sa ɗaya, sai dai kuma babban laifi ne idan sai da aka biya wanda zai bayar da ƙodar ta sa kuɗi, ko kuma aka ba shi wata lada daban.
Mai gabatar da ƙara ya shaida wa kotun cewa Ekweremadu ya biya yaron da aka so cirar ƙodar ya sa fam 7,000, sannan kuma aka yi masa alƙawarin za a kula da shi ya yi rayuwa cikin jin daɗi a Landan.
Shi dai wanda za a ciri ƙodar ta sa, bai san abin da aka yi niyyar yi da shi a Landan ba, har sai lokacin da ya yi ido huɗu da likita, wanda ya shaida masa cewa an kai shi ne asibitin domin a fafe cikin sa, a cire ƙodar sa ɗaya, a dasa wa ‘yar Ekweremadu.
Likitan ya ce yaron ya ji daɗi sosai da ya ji cewa tiyatar da za a yi masa ɗin ma ba za ta yiwu ba. Saboda dama bai san gaskiyar lamarin abin da ake ciki ba.
An ce an tafi da matashin Landan a matsayin ɗan’uwan Sonia Ekweremadu, alhali kuma babu wata dangantaka tsakanin su. Hakan bai sa likitoci sun amince su yi dashen ƙodar ba.
Su Ekweremadu Sun Yi Niyyar Illata Matashin – Mai Shari’a:
Mai Shari’a ya ce asibiti ya ce dashen ba zai yiwu ba, amma su Ekweremadu su ka haƙiƙice cewa ya cire ƙodar kawai daga jikin yaron, a ci gaba. Hakan a cewar Mai Shari’a, niyya ce ta illata yaron.
“Da an cire masa ƙoda, da ya ƙare rayuwar sa da ƙoda ɗaya, kuma ba shi da halin iya ɗaukar ɗawainiyar kula da lafiyar sa bayan cire masa ƙoda ɗaya.” Inji Mai Shari’a.
Ya ƙara da cewa ba a yi wa matashin yaron cikakken bayanin kasadar da zai iya faɗawa cikin ta ba.
A yanzu dai Sonia na Landan, kuma duk sati ana yi mata gashin ƙoda.
Mai gabatar da ƙara Joanne Jakymec ta ce abin da su Ekweremadu su ka nemi yi ƙeta ce, kuma sun nuna ba su ma damu da lafiya, rayuwa da jin daɗin yaron da su ka nemi a cire wa ƙoda ba.