Shugaba Bola Tinubu ya ce babu sauran batun wani abu wai shi tallafin fetur, domin a cikin Kasafin 2023 babu ma zancen kasafin a ciki.
Ya bayyana haka a lokacin jawabin sa na farko bayan rantsar da shi a Dandalin Eagle Square, Abuja.
An rantsar da Tinubu ƙarfe 10:37 na safiya.
Shi dai Kasafin 2023 ya na ɗauke da batun tallafin mai za a ci gaba da biya har cikin Yuni.
Tinubu ya ce kuɗaɗen tallafin fetur za a rika yi wa jama’a aiki da su, kamar gina ayyukan inganta ƙasa, kiwon lafiya, ilmi, samar da aikin yi da sauran su.
Mun yaba da matsayar da gwamnatin da ta tafi ta bayar na cire tallafin fetur, wanda masu hali ke ƙaruwa da kuɗaɗen ba talakawa ba. Tallafin fetur ba abu ne mai yiwuwa ba, a wannan lokacin da gwamnati ke fama da ƙarancin kuɗaɗe.
“Maimamkon biyan tallafin fetur, za mu riƙa karkata kuɗaɗen wajen yin ayyukan da zasu amfani jama’a baki ɗaya. Kamar kiwon lafiya, ilmi, samar da aikin yi da za inganta rayuwar miliyoyin ‘yan Najeriya,” cewar Tinubu.
Gwamnatin Buhari ta ce duk wata ta na kashe Naira biliyan 400 wajen biyan tallafin fetur.
Ta yi yunƙurin cire tallafin fetur amma sai daga baya ta bar lamarin ga gwamnatin Tinubu.
Discussion about this post