Babban Bankin Najeriya CBN ya janye lasisin bankunan al’umma guda 132, manyan bankunan bayar da lamuni guda hudu da wasu Kamfanonin bada rancen kudi guda uku.
CBN ya sanar da haka ne a shafinta dake yanar gizo ranar Talata.
Babban Bankin ya ce an soke lasisin cibiyoyin kudaden ne saboda sun daina gudanar da kasuwancin su a Najeriya wanda dama saboda hakan ne aka basu lasisin da zai yi aiki na tsawon watanni shida.
“An soke lasisin su ne saboda rashin kiyaye sharuddan da CBN ya bada bisa ga sashe na biyar na dokar bankuna BOFIA na shekarar 2020.
Manyan bankunan bada lamuni da aka soke lasisin su sun hada da Resort Savings & Loans, Safetrust Mortgage Bank, Adamawa Savings & Loans da Kogi Savings & Loans.
Kamfanonin bada rancen kudade da aka soke lasisin su sun hada da HHL Invest &Trust Limited, TFS Finance Limited da Trust Limited.
Sannan bankunan al’umman da CBN ta kwace lasisin su sun hada da Blue whales microfinance bank, Igangan Microfinance bank, Mainsail Microfinance Bank, Everest Microfinance Bank, Merit Microfinance Bank, Musharaka Microfinance Bank, Nopov Microfinance Bank da dai sauran su.
Discussion about this post