Babban Bankin Najeriya CBN ya ƙara kuɗin ruwa ga dukkan masu karɓar lamuni zuwa kashi 18.5% bisa 100% na adadin kuɗaɗen da za a karɓa.
An yi wannan wawan ƙari ne daga kashi 18% domin a magance tsadar rayuwa a cikin ƙasa.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ne ya bayyana ƙarin kuɗin ruwan a ranar Talata, bayan tashi taron da Kwamitin Tsare-tsaren Tattalin Arziki na CBN (MPC) ya tashi daga taro.
Yayin da ya ke wa manema labarai jawabi bayan tashi daga taron kwanaki biyu da ‘yan kwamitin MPC su ka yi, Emefiele ya ce kwamitin sun jefa ƙuri’ar amincewa a sa wa matsalar tsadar rayuwa sasari, sannan a kafa mata turke mai zurfin kashi 18.5% na kuɗaɗen ruwa, domin a hana tsadar rayuwa hauhawar ba-zatar da malejin tsadar ke yawan yi.
Sannan kuma Emefiele ya ce, mambobin kwamitin su 10 sun amince da tsarin, yayin da mamba guda ɗaya ya bayar da ta sa fatawar ta daban. Sai dai a ƙarshe duk an amince da tsadar rayuwa a bayanin Emefiele, tamkar kura ce, wadda ko an ɗaure ta da sarƙa da sasari, tilas kuma sai an maƙala mata takunkumi idan ana so a kwana lafiya.
Kwamitocin sun yi dogon zama a kan tsarin CRR, wato adadin kuɗaɗen da tilas sai kwastomomi sun ajiye a CBN, domin tabbatar da cewa sun cancanci karɓar lamunin da za su biya kuɗin ruwan na kashi 18.5%
Idan ba a manta ba, cikin Janairu CBN ya ƙara kuɗin ruwa daga kashi 16.5 zuwa kashi 17.5, don dai a hana tsadar kayan abinci da tsadar kayan masarufi yi wa talaka rumfa-sha-shirgi.
Sai kuma a cikin Maris bayan MPC sun tashi daga taron su, dai CBN ya ƙara kuɗin ruwa zuwa kashi 18%.
Discussion about this post