Yayin da ya rage saura kwanaki huɗu Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki, ya nemi amincewar Majalisar Dattawa domin ya biya wasu basussukan da ya ce na tara ne da kotuna daban-daban ta ci Gwamnatin Tarayya, amma ba a biya ba.
Buhari ya shaida wa Majalisar Dattawa a rubuce cewa kotuna daban-daban sun yanke hukuncin a biya kuɗaɗen wasu da naira, wasu fam na Ingila, wasu za a biya kuɗaɗen da dalar Amurka.
Ya ce kuɗaɗen sun ƙunshi dala 556,712,584; sai fam na Ingila 98,526,013; sai kuma naira 226,280,801,801.
Wannan roƙo na Buhari ya na cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ya karanta a zaman Majalisa na ranar Laraba.
A cikin wasiƙar, Shugaba Buhari ya bayyana cewa kuɗaɗen sun zama bashi ne a wuyan Najeriya, biyo bayan wasu ƙararrakin da aka kai ma’aikatun gwamnatin tarayya, cibiyoyi da hukumomin gwamnatin tarayya daban-daban, a kotunan daban-daban.
Ya ce Majalisar Zartaswa ce ta amince a biya kuɗaɗen tun a zaman ta na ranar 29 Ga Maris.
“Ina roƙon Majalisar Dattawa ta amince a biya wannan basussuka waɗanda duk hukunci ne da tarar da kotuna daban-daban ta ɗora wa Gwamnatin Tarayya, sakamakon wasu da su ka yi nasara kan ƙararrakin da su ka maka ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomin gwamnatin tarayya daban-daban.
Daga nan sai Shugaba Buhari ya nemi Majalisar Dattawa ta tuntuɓi Antoni Janar da Ma’aikatar Kasafin Kuɗaɗe da Tsare-tsare, domin samun ƙarin haske dangane da basussukan.
Buhari nemi biyan waɗannan basussuka mako ɗaya bayan ya nemi iznin Majalisar Dattawa ya ciwo bashin dala miliyan 800.