Ɗan takarar gwamnan Jihar Ogun ƙarƙashin PDP, Ladi Adebutu ya maka Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami kotu. Ya maka shi ne kotu tare da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda na Najeriya, Usman Baba da kuma jam’iyyar APC, bayan fitar labarin da PREMIUM TIMES ta buga, inda ta buga abin da binciken ‘yan sanda ya ƙunsa, dangane da zargin sayen ƙuri’u na Naira biliyan 2 da ake zargin Adebutu ya yi, ta hanyar katin ATM a ranar zaɓe.
Haka nan kuma Adebutu ya maka Shugaban SSS na Kasa, Yusuf Bichi kotu da Shugaban EFCC, Abdulrashid Bawa, duk saboda zargin sayen ƙuri’u da aka yi masa.
Ba su ke nan ba, ya haɗa da Shugaban APC na Jihar Ogun, Yemi Sanusi duk ya maka su kotu.
Sanusi dai shi ne ya rubuta wasiƙar ƙorafi ga Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, ya nemi a binciki Adebutu, saboda ya raba katin ATM wanda aka loda wa kuɗaɗe a ranar zaɓe kuma a rumfunan zaɓen jihar.
Adebutu ya maka su ƙara sa’o’i 12 bayan PREMIUM TIMES ta buga labarin zargin sa da ‘yan sanda ke yi. Tuni kwafen takardun ƙarar da ya shigar sun shigo hannun PREMIUM TIMES, ta dafe.
A ƙarar da Adebutu ya shigar, ya bayyana wa kotu cewa tun da farko APC ta kai ƙorafi ga Ministan Shari’a Abubakar Malami da EFCC, kuma daga nan ne ‘yan sanda su ka gayyace shi, amma da niyyar idan ya je su damƙe shi, don kawai su hana shi ko su karkatar da shi daga ƙarar Gwamna Dapo Abiodun a Kotun Ɗaukaka Ƙara.
Adebutu ya shaida wa kotu cewa ya na roƙon ta hana Minista Malami, ‘Yan Sanda, EFCC da SSS kama shi.
Ya ce su na son kama shi ne kawai don su hana shi shari’ar ƙarar da ya maka Gwamna Abiodun na APC, wanda ya yi nasara kan sa a zaɓen da ratar ƙuri’u 14,000 kaɗai. Adebutu na PDP dai ya ce an yi masa maguɗi shi ya sa ya maka Abiodun kotu.
A cikin kwafen ƙarar da Adebutu ya shigar, ya na so kotu ta bayyana cewa, tunda ya maka Gwamna Abiodun ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara kan zaɓen gwamnan Jihar Ogun ɗin, don haka bai halasta ‘Yan Sanda, EFCC ko SSS su kama shi ba. Idan aka yi haka, tan tauye masa haƙƙi kenan.
Asalin Dambarwar: