1. Shin an taɓa kama Bola Tinubu da harƙallar safarar muggan ƙwayoyi a Amurka, cikin 1993 ko ba a kama shi ba?
2. Shin da aka kama shi, an gurfanar da shi kotu, ko ba a gurfanar da shi kotu ba?
3. Shin da aka maka shi Kotun Gundumar Illinois ta Amurka, an same shi da laifi har aka ƙwace $460,000 a asusun ajiyar sa na banki, ko kuwa hakan bai faru ba?
4. Me dokar Najeriya ta ce dangane da mai irin wannan laifin idan ya nemi tsayawa takara, musamman ta zaɓen shugaban ƙasa?
5. Shin Bola Tinubu ya ci kashi 25 bisa 100 na yawan ƙuri’un da aka jefa a FCT Abuja a zaɓen shugaban ƙasa?
6. Idan Tinubu bai ci kashi 25 a FCT Abuja ba, me doka ta ce a kan haka?
7. Shin ta tabbata Tinubu ya yi satifiket na bogi ko bai yi ba?
8. Idan ya yi satifiket na bogi, me doka ta ce a kan haka, kan wanda zai yi takarar muƙamin siyasa?
9. Shin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta karya ƙa’idar da ta shimfiɗa wajen tsarin tattara sakamakon zaɓe, ko ba ta karya ba?
10. Shin sunan Kashim Shettima ya fito a wurin takara biyu ko bai fito ba, wato ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa da kuma ɗan takarar sanata a Jihar Barno?
11. Shin akwai harƙalla a tattara sakamakon zaɓe ko babu?
12. Shin laifukan da Peter Obi da LP ke zargin Tinubu ya aikata, idan sun tabbata ya aikata ɗin, cin amanar ƙasa ce ko ba cin amanar ƙasa ba ce?