Kanawa da sauran matafiya da Zazzagawa da al’ummar Kaduna ba za su manta da mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ba, saboda namijin ƙoƙarin da ya yi wajen gyara titin Kano zuwa Kaduna.
Titin ya shafe shekaru masu yawa ya na cin rayukan ɗimbin matafiya saboda tsananin lalacewar da ya yi. A kullum ana asarar rayuka da kayayyaki na miliyoyin nairori sanadiyyar haɗurran da aka riƙa yi kan titin mai tsawon kilomita 226.
Gyara titin da aka yi ya kawo sauƙin zirga-zirga da kuma karakainar ababen hawa. Duk da dai akwai ɗan ƙarashen da ba a kammala ba baki ɗaya ba.
Kalubalen da Buhari zai sauka ya bari shi ne yadda za a kammala gyara titin daga Kaduna zuwa Abuja, wanda a bisa dukkan alamu, za a daɗe kafin a kai gaci.