Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa da gangar ya sa aka rufe iyakokin kasar nan saboda ƴan Najeriya su rungumi garma kowa ya noma abinda zai ci da iyalan sa.
Yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da sabon ginin Hedikwatar hukuma Kwastam ta kasa a Abuja, Buhari ya kara da cewa, saboda haka ne ya nada mutum irin Hamid Ali domin ya tsaftace iayakokin kasar nan saboda fasakwauri.
” Saboda kowa yana so ya burge makwabcin sa ko wani na kusa dashi, ba zai ci shin kafar gida na sai ta waje. Da muka hana shigowa da shinkafar ba gashi kowa ya koma gina ba.
” Yanzu muna noma abincin da za mu ciyar da kan mu tunda Allah ya azurta mu da kasar noma da kuma al’umma.
” Daga farko ana ta sukar mu amma daga baya fa, an yi ta yaba mana saboda kwazon da muka yi da kuma jajircewa akan cewa lallai ba za a shigo maba da shinkafar waje ba.
Da yake magana game da sauran kwanakin da suka rage masa a fadar shugaban kasa, Bugary ya Ce ” Saura min kwanaki shida kacal in sallama da Aso Rock. Zan koma Daura in yi zama na can, dama kuma ta yi nesa da Abuja. Idan wasu suka nemi su takura min a can din ma dam aina da kyakkyawar alaka da kasar Nijar, na san za su kawo min ɗauki.
Discussion about this post