Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF), ya nuna damuwar sa, ganin yadda kashi 98.5 na ‘yan Najeriya da su ka su ka shiga Manhajar Asusun eNaira, duk sun yi watsi da tsarin kwata-kwata.
IMF ya nuna wannan damuwar a cikin wata takardar da ya fitar kwanan nan, mai ɗauke da rahoton: ‘Nazarin Tsarin eNaira A Najeriya, Bayan Shekara Ɗaya Da Kafawa.’
A cikin rahoton, IMF ya yi nazarin matsayar da tsarin na eNaira ya ke a yanzu bayan shekara ɗaya da kafawa, tare da cewa kwata-kwata jama’a ba su rungumi shirin ba, sai ɗan abin da ba a rasa ba.
IMF dai na ƙoƙarin ta nuna cewa a cikin mutum 100, mutum ɗaya ne tal ya rungumi tsarin.
“Idan za a auna hada-hadar kuɗaɗen da aka yi ta hanyar tsarin eNaira tun daga ranar da aka kafa tsarin, za a cewa bai fi sau 14,000 ake amfanin da tsarin a kowane mako. Hakan ya na nufin kashi 1.5 kaɗai na masu Asusun eNaira ke amfani da shi. Kenan kashi 98.5 na masu ‘eNaira Wallets’, duk sun yi watsi da tsarin. Kusan ma ko sau ɗaya waɗannan kashi 98.5 ɗin ba su yi amfani da na su ba.” Haka dai rahoton na IMF ya jaddada.
“Wato a farkon fito da tsarin, an kwashi asusun walet har 500,000 a cikin kwanaki 25. Amma kafin yawan ya kai 600,000, sai da aka shafe kwanaki 63. Kuma sai da aka kwana 143 sannan aka kai walet 700,000.” Cewar IMF.
“Zuwa ƙarshen Nuwamba 2021 akwai asusun eNaira walet 860,000. Kun ga adadin bai ma kai kashi 1 na yawan asusun bankuna da ke ƙasar nan ba.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya ƙaddamar da Shirin eNaira na CBN a ranar 25 ga Oktoba, 2021, a Abuja.
Discussion about this post