Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya ce masharranta da algungumai ne ke neman haɗa shi gaba da Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu da kuma ɗaya daga cikin jigon APC, Ibrahim Masari.
Kwamishinan Yaɗa Labaran Kano, Garba Mohammed ya bayyana haka a ciki wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Sanarwar dai ta biyo bayan fitar wata murya wadda Ganduje ke zantawa da Ibrahim Masari, inda su ke gulmar Bola Tinubu, saboda ya yi ganawa ta musamman da jagoran Kwankwasiyya, Rabi’u Kwankwaso, a Paris cikin makon da ya gabata.
A cikin muryar wadda aka naɗa daga wayar tarho tsakanin Masari da Ganduje, an ji Ganduje a cikin murya mai sanyi da ban-tausayi ya na nuna rashin jin daɗin sa dangane da yadda Tinubu ke ta ƙoƙarin rungumar Kwankwaso, har ya na ƙoƙarin shigar da shi cikin gwamnatin sa wadda za a rantsar nan da kwanaki takwas.
Ganduje ƙarara ya bayyana wa Masari rashin jin daɗin yadda Tinubu ya yakice shi, ya maida shi na-ware-da-dangi.
Sai dai kuma da ya ke raddi a madadin Ganduje, Kwamishinan Yaɗa Labaran Kano, Muhammad Garba, ya bayyana cewa magulmata sun ruruta maganganun na Ganduje domin jama’a da dama su yi abin da ya furta.
Garba ya ce wasu magauta ne da aka biya su ka yayata muryar domin su haddasa rashin jituwa tsakanin Ganduje, Ibrahim Masari da Tinubu.
“A bisa dukkan alamu wasu mutane ne waɗanda su ka maida hankali wajen ganin sun haddasa rashin fahimta tsakanin Tinubu, Ibrahim Masari da Ganduje su ka watsa muryar har kowa ya ji.
Ya ce maganganun ba su kai nauyin a ba su muhimmancin da har za a riƙa watsa su ba. Amma saboda wata nifaƙar biyan buƙatar wasu, sai su ka maida hankali a kan muryar.
“To tuni dai Gwamna Ganduje da Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa sun fahimci wasu algungumai ne su ka yi ƙoƙarin cusa ƙiyayya da saɓani a tsakanin su.”
Garba ya ce “Tinubu da Ganduje ba za su bayar da ƙofar har wasu ɗibgaggu su cusa rashin fahimta ko saɓani ya lalata kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin su, musamman ma a irin wannan hali da ake ciki.”
A cikin muryar dai Masari ne ya fara ce wa Ganduje ai ya faɗa masa abin da ke faruwa tsakanin Tinubu da Kwankwaso.
Ganduje a cikin damuwa da mamaki ya riƙa cewa saboda an ga su yanzu babu gwamnati a hannun sa, shi ya sa Tinubu zai tattago Kwankwaso.
Discussion about this post