Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya yi alƙawarin yi wa ƙasa ayyukan ci gaba daidai-wa daidai ba tare da nuna wariya ga wani ɓangare ba.
Tinubu, wanda za a rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa a ranar 29 ga Mayu, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a garin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.
A takardar sanarwa wanda ofishin watsa labarai na zaɓaɓɓen shugaban kasar ta fitar, kuma AbdulAziz AbdulAziz ya saka wa hannu, Tinubu yana ziyarar kwanaki biyu ne a jihar domin ƙaddamar da ayyukan da gwamnatin Nyesom Wike ta aiwatar.
“Ba zan mayar da wani yanki saniyar ware ba, amma zan bar ayyukan da ba za a manta da su ba a faɗin Nsjeriya,” in ji shi a yayin buɗe gadar Rumuokwuta/Rumuola.
Tinubu ya yaba wa Gwamna Wike bisa ayyukan ci gaba da ya aiwatar a jihar Ribas, musamman gadar sama har 12 da aka gina a faɗin babban birnin jihar, inda ya ce lallai tarihi zai riƙa tunawa da shi.
Ya ce da irin nasarorin da ya samu a jihar, Najeriya za ta buƙaci gwamnan Ribas ɗin mai barin gado a manyan muƙamai.
A ɓangaren siyasa, Tinubu ya godewa Wike da al’ummar jihar Ribas bisa goyon bayan da suka ba shi.
Ya ce yana jihar ne bisa alƙawarin da ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓe a Ribas, inda ya ce “idan ka yi alƙawari, ka cika shi.
“Ba zan taɓa mantawa da muhimmiyar rawar da manya da kuma al’ummar jihar nan suka taka ba a yaƙin neman zaɓen da na yi na zama shugaban ƙasar nan. Kuna da godiyata ta har abada.
“A mai girma Gwamna Wike, na ga mutum mai ƙa’ida. Ya ɗauki matakin da ya dace na cewa a mayar da shugabancin ƙasarnan Kudu, kuma ya samu ƙwarin guiwar jajircewa kan matsayarsa, ba tare da la’akari da wa hakan zai ɓatawa ba.
“Haƙiƙa shi mutum ne mai mutunci. Bai zaɓi biyan buƙatar kansa ba, a’a, ya zaɓi biyan buƙatar ƙasa da al’ummar jihar Ribas, ina gode masa bisa wannan jagorancin na sadaukar da kai,” inji shi.
A nasa jawabin, Wike ya ce gayyatar da aka yi wa Tinubu domin ƙaddamar da ayyuka a jihar cika alƙawari ne da aka yi a ziyarar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a Ribas.
Ya kuma godewa Tinubu kan yadda ya amince ya ziyarci jihar Ribas tare da ƙaddamar da ayyukan.
Wike, wanda ya caccaki shugabannin jam’iyyarsa ta PDP, ya yaba da zaɓen Tinubu wanda a cewarsa, ya kunyata masu zagon ƙasa.
Taron ya samu halartar Kakakin majalisar wakilai Hon. Femi Gbajabiamila da Gwamna Abubakar Badaru (Jigawa), David Umahi (Ebonyi), Abdulrahman Abdulrazaq (Kwara), Seyi Makinde (Oyo) da Hope Uzodinma (Imo).
Sauran sun haɗa da tsoffin gwamnoni Dr Peter Odili (Ribas), Cif Bisi Akande (Osun), Cif James Ibori (Delta), Dr Kayode Fayemi (Ekiti), Cif Timipre Sylva (Bayelsa) da Cif Ayo Fayose (Ekiti).
Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da zaɓaɓɓen gwamnan jihar Ribas, Sim Fubara, Ministan matasa da ci gaban wasanni, Sunday Dare, Dele Alake da kuma Kashim Imam, da dai sauransu.
Discussion about this post